Dadi ya kashe tsohon shugaban yakin neman zaben Tinubu bayan hadewa da Kwankwaso a siyasa

Dadi ya kashe tsohon shugaban yakin neman zaben Tinubu bayan hadewa da Kwankwaso a siyasa

  • Hon. Abdulmumin Jibrin ya fito shafin Facebook ya na nuna farin cikinsa bayan ya sauya-sheka
  • Abdulmumin Jibrin da ya fice daga APC zuwa jam’iyyar NNPP ya ce sai yanzu ya samu natsuwa
  • Tsohon ‘dan majalisar ya nuna yanzu yake iya barci da duka idanunsu a rufe da ya fice daga APC

Kano - Yayin da siyasar Kano ke canza salo, a karon farko a cikin shekaru bakwai, Abdulmumin Jibrin ya bayyana cewa ya samu barcinsa mai kyau.

Hon. Abdulmumin Jibrin ya bayyana wannan a shafinsa na Facebook, jim kadan bayan shi da wasu ‘yan siyasa sun zauna da Rabiu Musa Kwankwaso.

Tsohon ‘dan majalisar tarayyar na Kiru/Bebeji ya ce yanzu rayuwarsa ta fara komawa daidai.

“Na godewa Ubangiji SWT, a karon farko a cikin shekaru bakwai, zan iya yin barci da idanuna biyu a rufe.”

Kara karanta wannan

2023: Tambuwal ya tona ‘Dan Arewan da APC ta ke shirin ta tsaida takarar Shugaban kasa

“Tare da samun natsuwar zuciya, kwanciyar hankali da farin ciki. Bari in cigaba da rayuwa ta daga inda ta tsaya.”
“Wasu darasin da karfi da yaji ake koyansu a rayuwa.” - Hon. Abdulmumin Jibrin

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tsohon Sarkin yakin neman zaben Bola Tinubu
Abdulmumin Jibrin da Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: abdulmuminjib
Asali: Facebook

A karshe Jibrin ya karasa da cewa:

“Alhamdulillah Kwanciyar hankali...
Allah na gode, na gode na gode...”

- Hon. Abdulmumin Jibrin.

Legit.ng Hausa ta fahimci Hon. Jibrin wanda ya dawo jam’iyyar hamayya ta NNPP kwanan nan ya zauna da tsohon gwamna Rabiu Musa Kwankwaso.

An ga tsohon ‘dan majalisar tarayyar tare da jiga-jigan Kwankwasiyya a gidan jagoran tafiyar ta su.

Ziyara zuwa gidan Shekarau

Daga baya Jibrin da wasu manyan kusoshin NNPP a jihar Kano sun ziyarci gidan tsohon gwamna watau Malam Ibrahim Shekarau domin yi masa maraba.

Tawagar tsohon Gwamna Kwankwaso da ta je gidan Sanata Shekarau ta hada da Kawu Sumaila, Abba Kabir Yusuf, da kuma Ahmad Abdussalam Gwarzo.

Kara karanta wannan

Kwankwasiyya ta samu karuwa, shugaban yakin neman zaben Tinubu ya rungumi NNPP

Ragowar su ne: Dr. Abdullahi Garba Bichi, Kabiru Alhassan Rurum da shi Abdulmumin Jibrin.

Rikicin Garo da Barau ya cabe

Kun samu labari ana cigaba da samun rikici tsakanin kusoshin APC na Kano. Murtala Sule Garo bai ji dadin sasantawar da Gwamna ya yi da Barau Jibrin ba.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya sasanta da ‘yan bangaren Barau Ibrahim Jibrin, ta hanyar janye takarar Sanatansa, hakan ya batawa wasu 'yan APC lissafi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng