Taron siyasa a Plateau: Atiku ya ba da hakuri bisa fatattakar 'yan jarida da ya yi

Taron siyasa a Plateau: Atiku ya ba da hakuri bisa fatattakar 'yan jarida da ya yi

  • Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya baiwa yan jarida hakuri a kan sabani da suka samu a taron ganawa da wakilan PDP a jihar Plateau
  • Mai neman takarar shugaban kasar a karkashin inuwar jam'iyyar PDP ya ce an yi masa mummunar fahimta ne amma ko shakka babu yan jarida na cikin ajandarsa
  • Mun dai ji a baya cewa an fatattaki wasu yan jarida a yayin ziyarar da Atiku ya kai sakatariyar PDP a garin Jos a ranar Litinin, 16 ga watan Mayu, don ganawa da wakilan jam'iyyar a jihar

Plateau - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya nemi afuwar yan jarida a jihar Plateau kan harin da jami’an tsaro suka kai masu.

An tattaro cewa an fatattaki wasu yan jarida a yayin ziyarar da Atiku ya kai sakatariyar PDP a garin Jos a ranar Litinin, 16 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

2023: Atiku Ya Fatattaki Ƴan Jarida Daga Sakatariyar PDP Ta Plateau

Taron siyasa a Plateau: Atiku ya ba da hakuri bisa hana 'yan jarida yin aikinsu
Taron siyasa a Plateau: Atiku ya ba da hakuri bisa hana 'yan jarida yin aikinsu Hoto: Punch
Asali: Facebook

Legit Hausa ta kawo cewa tsohon mataimakin shugaban kasar ya isa sakatariyar ta PDP na Plateau da misalin karfe 2.19 na rana, amma da ya tarar da yan jarida suna jiransa, ya bada umurnin su fita yana cewa "ba abin da ya hada ni da yan jarida". Deleget na zo gani.”

Wannan umurnin ya saka hadimansa da jami'an tsaronsu suka bazama suka fara fatattakar yan jaridar, hakan ya janyo turereniya, aka yi asarar na'urori ciki har da wayar salula da sandar dora kwamara ta Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin wata sanarwa a ranar Talata, Atiku ya bayar da hakuri kan lamarin, yana mai cewa ba zai iya bayar da umurnin cewa a toshe kafafen watsa labarai daga taron ba.

Shugaban kwamitin takarar shugabancin Atiku na 2023, Cif Raymond Dokpesi, wanda ya sanya hannu kan sanarwar a madadin ubangidansa ya karyata rahotannin kafafen watsa labarai cewa an hana yan jarida daukar taron tattaunawar Atiku da wakilan PDP wanda aka yi a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Daga Ƙarshe, Adesina Ya Yi Magana Kan Batun Takarar Shugaban Ƙasa a 2023

Dokpesi ya bayyana cewa abin da ya faru shi ne:

"Lokacin da ya isa sakatariyar jam’iyyar PDP ta jihar Plateau da ke Jos inda tsohon mataimakin shugaban kasar zai gana da wakilai daga cikin tuntubar da yake yi gabanin babban taron jam’iyyar na kasa da za a yi a ranar 28 ga watan Mayu, a bayyane yake cewa tuni ‘yan jarida suka shiga dakin taron da yawansu kuma cewa yana so ya gana da wakilan daban kafin ya zanta da su."

Ya ce kawai dan takarar shugaban kasar ya roki yan jarida ne kan su basu wuri, sannan su dawo don hira bayan sun kammala tattaunawa sannan kuma ya bayar da hakuri kan yanayin da jami’an tsaro suka tafiyar da lamarin.

Shugaban kwamitin ya roki yan jarida da kada su yiwa manufar tsohon mataimakin shugaban kasar mummunan fassara, yana mai cewa kafofin watsa labarai na cikin ajandarsa, rahoton Thisday.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Amaechi ya yi murabus daga majalisar Buhari, Malami ya yi biris da umurnin ubangidansa

2023: Atiku Ya Fatattaki Ƴan Jarida Daga Sakatariyar PDP Ta Plateau

Mun kawo a baya cewa Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa a zaben 2023 a PDP ya umurci hadimansa da jami'ansa tsaro su fatattaki yan jarida daga dakin taro a sakariyar PDP a Plateau.

Atiku ya ce shi deleget ya zo gani da 'yan jarida ba don haka hadimansa da jami'an tsaro suka fattaki yan jaridar har wasu suka lalata wayoyinsu da kayan aiki wurin turereniya garin tserewa.

Yan takarar shugaban kasa da dama sun ziyarci Jihar ta Plateau amma duk cikinsu babu wanda ya umurci a kori yan jarida a yayin da ya zo gana wa da deleget da shugabannin jam'iyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng