Yadda Jam’iyyar APC ta samu tayi wa Yari, Marafa da Gwamna Matawalle sulhu a Zamfara
- Ganin 2023 ya karaso, uwar jam’iyya ta yi wa dukkanin shugabanni da jagororin APC sulhu a Zamfara
- An ware wasu kujerun da aka ba bangaren su Yari domin a samu zaman lafiya da Gwamna mai-ci
- Jam’iyyar APC ta hada-kan mutanen Yariman Bakura, Shinkafi, Yari, Marafa da tsagin Matawalle
Zamfara - Bangarorin jam’iyyar APC mai mulki a jihar Zamfara sun gudanar da gangami na musamman don tabbatar da dinke barakar da ake da ita.
Jaridar Daily Trust ta ce wannan gangami da aka shirya ya nuna an kawo karshen rikicin cikin gidan da aka dauki lokaci ana fama da shi a jam’iyyar.
An yi taron ne a filin wasan Ahmadu Bello da ke garin Gusau. Kusan duka manyan jagororin APC sun samu halartar wannan fitowa da aka yi a ranar Litinin.
Mai girma Gwamna Bello Muhammad Matawalle yana cikin wadanda aka gani a wajen taron.
Sauran jiga-jigan APC da suka tofawa tafiyar albarka su ne tsofaffin gwamnoni: Ahmad Sani Yarima, Mahmud Aliyu Shinkafi, sai Abdulazeez Yari.
Hadimin Gwamnan jihar Zamfara, Zailani Bappah ya ce Hassan Mohammed Nasiha, Kabiru Marafa, Dansadau, da Sahabi Yau sun halarci gangamin.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An raba kujerun takara a APC
Duka wadanda aka gani a wajen sun nuna goyon bayansu ga yin sulhu, tare da kira ga mabiyansu da su ajiye sabanin da aka samu a baya, su tari gaba.
A wani rahoton da ya fito daga Daily Telegraph, an ji cewa Mai girma Bello Matawale ya yarda a ba ‘yan tsagin Abdulaziz Yari wasu kujeru masu tsoka.
Saboda a zauna lafiya a APC ne Bello Matawale ya sa hannu cewa a bar wa bangaren Yari takarar Sanatoci biyu da ‘yan majalisar wakilan tarayya hudu.
A gefe guda, mutanen tsohon gwamnan za su marawa Matawalle baya domin ya zarce a 2023. Wannan sulhu zai ba shi damar samun tikiti cikin sauki.
Wata majiya ta shaidawa jaridar cewa an cin ma matsaya za a bar wa bangaren gwamna takarar Sanata daya da kuma ‘yan majalisar wakilan tarayya uku.
Sulhu a Kano
A irin haka ne aka ji labari Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ba zai nemi kujerar Majalisar Dattawa a Kano a zabe mai zuwa ba, duk da ya saye fam.
Dr. Abdullahi Ganduje ya hakura Barau Ibrahim Jibrin ya sake yin takara a jam’iyyar APC mai mulki a dalilin wani sulhu da aka yi a makon da ya wuce.
Asali: Legit.ng