'Yan majalisar Kaduna: Burin El-Rufa'i ya koma rayuwar kasar waje bayan mulkinsa

'Yan majalisar Kaduna: Burin El-Rufa'i ya koma rayuwar kasar waje bayan mulkinsa

  • 'Yan majalisa a jihar Kaduna sun roki Tinubu ya zabi El-Rufai a matsayin abokin gami a zaben 2023 mai zuwa
  • Majalisar ta bayyana hakan ne ga Tinubu domin kange gwamnan daga kauracewa Najeriya bayan sauka a mulki
  • A bangare guda, Tinubu ya bayyana kwarin gwiwar shi zai gaji Buhari a zabe mai zuwa na 2023 idan Allah ya kaimu

Kaduna - Mambobin Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Kaduna sun roki babban jagoran su na kasa, Asiwaju Bola Tinubu da ya zabi gwamnan jihar, Mallam Nasir El-Rufai a matsayin abokin takararsa a zaben shugaban kasa na 2023.

A makon da ya gabata ne Tinubu ya ziyarci Kaduna don zawarcin kuri’un wakilan APC 69 a jihar gabannin zaben fidda gwani na jam’iyyar, inji rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Buhari fa na da dan takarar da yake so ya gaje shi, Adesina ya magantu

El-Rufai zai bar Najeriya bayan mulkinsa
'Yan majalisar Kaduna: Burin El-Rufa'i ya koma rayuwar kasar waje bayan mulkinsa | Hoto: punchng.com
Asali: Twitter

Mai neman takarar shugaban kasar ya fadama wakilan cewa yana da karfin gwiwar cewa shine zai zama shugaban kasa na gaba idan Muhammadu Buhari ya sauka a shekara mai zuwa.

Tinubu ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Wasu na takara, ban san ina suke zuwa ba amma ni Villa za ni.”

Kan haka, gaba daya wakilan APC a Kaduna sun lamuncewa Tinubu, yayinda jam’iyyar reshen jihar suka roke shi da ya zabi El-Rufai a matsayin abokin takara.

Da yake magana a madadin wakilan Kaduna, dan majalisa mai wakiltan Sabon Gari, Garba Babawo, ya roki Tinubu da ya dauki El-Rufai a matsayin abokin takararsa.

Babawo ya ce:

“Muna da wata bukata a gare ka (Tinubu), yallabai. Abun da nake shirin fadi, ban fadawa gwamnanmu ba saboda na san idan na fada masa ba zai goyi bayan haka ba. Muna so ka dauki gwamnanmu a matsayin abokin takararka.

Kara karanta wannan

Duk mu na goyon bayan Bola Tinubu a zaben Shugaban kasa – El-Rufai ya dauki matsaya

“Ba ma so ya koma wajen kasar da zama bayan zaben domin mun san shirinsa. Shirinsa shine barin kasar da komawa kasar waje da zama bayan kammala wa’adinsa a matsayin gwamna. Amma muna so ya yiwa kasar hidima a matsayin abokin takararka.”

A jawabinsa a taron, tsohon gwamnan jihar Borno, Sanata Kashim Shettima, ya ce Tinubu na da duk abubuwan da tsoffin Shugabannin kasar ke da shi, musamman karamci da son zaman lafiya irin na Janar Yakubu Gowon.

Bidiyon Kwankwaso Ya Isa Gidan Shekarau Don 'Ƙarasa' Maganan Komawarsa NNPP

A wani labarin, tsohon gwamnan Kano kuma jagoran jam'iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso ya isa gidan Ibrahim Shekarau, sanatan Kano ta Tsakiya.

Wata bidiyo da Daily Trust ta wallafa ya nuna Kwankwaso yayin da dira gidan na Shekarau cikin wata baƙar mota sanye da fararen tufafi da jar hula kamar yadda aka saba ganinsa.

Magoya baya da dama sun taru kofar gidan na Shekarau inda suka riƙa yi wa Kwankwaso maraba kafin daga bisani Shekarau ya fito ya tarbe shi kuma suka shiga gida tare.

Kara karanta wannan

Babu abin da zai hana PDP karbe mulkin Najeriya a 2023, In ji Ayu

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng