Yanzu-Yanzu: Bidiyon Kwankwaso Ya Isa Gidan Shekarau Don 'Ƙarasa' Maganan Komawarsa NNPP

Yanzu-Yanzu: Bidiyon Kwankwaso Ya Isa Gidan Shekarau Don 'Ƙarasa' Maganan Komawarsa NNPP

Kano - Tsohon gwamnan Kano kuma jagoran jam'iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso ya isa gidan Ibrahim Shekarau, sanatan Kano ta Tsakiya.

Wata bidiyo da Daily Trust ta wallafa ya nuna Kwankwaso yayin da dira gidan na Shekarau cikin wata baƙar mota sanye da fararen tufafi da jar hula kamar yadda aka saba ganinsa.

Yanzu-Yanzu: Bidiyon Kwankwaso Ya Isa Gidan Shekarau Don Ƙarasa Maganan Komawarsa NNPP
Bidiyon Kwankwaso Ya Isa Gidan Shekarau Don Ƙarasa Maganan Komawarsa NNPP. Hoto: @salisuauwal123
Asali: Twitter

Magoya baya da dama sun taru kofar gidan na Shekarau inda suka riƙa yi wa Kwankwaso maraba kafin daga bisani Shekarau ya fito ya tarbe shi kuma suka shiga gida tare.

Ana kyautata tsamanin cewa Kwankwason ya kai ziyarar ne domin ƙarasa tattauna batun komawar Shekarau jam'iyyar NNPP mai kayan marmari.

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Ganduje bai sani yin takarar sanatan Kano ta tsakiya ba, yin kaina ne - Lado

A baya-bayan nan dai yan jam'iyyar APC da dama a Kano sun riƙa fita suna koma wa NNPP gabanin babban zaben 2023.

Jam'iyyar APC ta kasa ta yi yunkurin ganin anyi sulhu da Shekarau ya cigaba da zama a APC har a baya-bayan nan aka tura Gwamna Ganduje ya gayyace shi zuwa Abuja amma tafiyar ba ta yi wu ba.

Wasu na kusa da Shekarau din sun tabbatar da cewa a halin yanzu fa batu ya yi nisa mallam ƙiris dama ta rage ya sanar da komawarsa NNPP.

Saurari karin bayani...

Asali: Legit.ng

Online view pixel