Yanzu-Yanzu: Ganduje Ya Dira Gidan Shekarau 'Don Ƙoƙarin Hana Shi Fita Daga APC'
- Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya tafi gidan Sanata Ibrahim Shekarau a Kano inda suka shiga suka yi gannawar sirri a yau Juma'a
- Amma wasu majiyoyi na kusa da Shekarau sun ce Ganduje ya kai masa ziyarar ne don shawo kansa kada ya bi Kwankwaso zuwa jam'iyyar NNPP
- Yan majalisu na Kano a baya-bayan nan sun rika fita daga jam'iyyar APC suna koma wa NNPP kan dalilai da suka shafi rikicin cikin gida da rashin adalci ds
Jihar Kano - Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano ya ziyarci sanata mai wakiltar Kano Central, Mallam Ibrahim Shekarau a gidansa.
Daily Trust ta rahoto cewa tsohon gwamnan (Shekarau) ya kammala shirin koma wa jam'iyyar New Nigeria Peoples Party, NNPP, a ranar Asabar saboda rikicin Jam'iyyar APC a Kano.
Tsaffin gwamnonin biyu sun yi taron sirri a gidan Shekarau a yammacin ranar Juma'a.
Duk da ba a bayyana abin da suka tattauna ba yanzu, majiyoyi na kusa da tsohon gwamnan sun ce Ganduje ya zo ya dakatar da fita daga APC da Shekarau ke niyyar yi zuwa NNPP ne, wacce wani tsohon gwamna jihar, Rabiu Musa Kwankwaso ke yi wa jagoranci.
"Yanzu ya tafi. Sun shiga cikin gida sun tattauna, amma babu wanda ya san ainihin abin da suka tattauna," majiyar ta kara da cewa.
Daily Trust ta rahoto cewa Kwankwaso ya isa Kano a ranar Juma'a a cikin shirye-shiryen tarbar Shekarau zuwa NNPP.
Saurari karin bayani ...
Asali: Legit.ng