Shirin 2023: Buhari fa na da dan takarar da yake so ya gaje shi, Adesina ya magantu
- Hadimin shugaba Buhari ya bayyana matsayin shugaban kasa kan zaben 2023 mai zuwa da ake ci gaba da shiri akai
- Ya bayyana cewa, shugaba Buhari na da dan takarar da yake so, amma ba zai ambaci sunansa ba a yanzu tukuna
- Hakazalika, Adesina ya bayyana abin da zai yi idan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauka a zaben 2023
Abuja - Mai bawa shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara na musamman kan harkokin yada labarai Femi Adesina, ya ce shugaba Buhari na da wanda ya fi son ya gaje shi a 2023, amma ba zai ambaci sunan mutumin ba.
Adesina ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Channels TV’s Politics a jiya Alhamis.
Ya zuwa yanzu dai ministoci Abubakar Malami, Rotimi Amaechi, Godswill Akpabio, Chris Ngige, Ogbonnaya Onu da karamin minista a ma’aikatar ilimi, Emeka Nwajiuba sun shiga takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC.
Adesina, wanda ya ce shi ba dan jam’iyyar APC ba ne mai dauke da katin jam'iyya, ya tabo batun yajin aikin ASUU, da kuma yadda shugaban kasar ke da muradin warware matsalar.
Daily Post ta ruwaito shi yana magana kan abin da zai yi bayan saukar shugaba Buhari, Adesina ya ce:
"Guduwa gidana zan yi. Eh na zabi in gudu gida bayan kammala aiki na.”
Adesina ya ce:
“A wata hira da aka yi da shi a baya da aka tambayi shugaban kasar ko yana da wanda ya fi so, ya amsa da cewa akwai; amma ba zai ambace shi ba domin komai zai iya faruwa da shi.
“Hakan ya nuna maka cewa shi kansa shugaban kasa yana da sha’awar tafiyar kuma yana da wanda ya fi so; amma ko zai dora dan takararsa shine abin da ba za ka iya tantancewa a halin yanzu ba."
Sai dai Adesina ya ce duba umarnin shugaban kasar na baya-bayan nan na cewa masu rike da mukaman siyasa su yi murabus kafin ranar 16 ga Mayu, shugaban na iya yanke shawarar cike wasu mukamai idan wasu ministoci suka yi murabus.
Gwarzon Dimokradiyya: Za a karrama shugaba Buhari da babbar lambar yabo
A wani labarin, nan ba da jimawa ba za a karrama shugaban kasa Muhammadu Buhari da lambar yabo ta gwarzon dimokuradiyya, wanda majalisar ba da shawara ta jam’iyyu (IPAC) za ta ba shi.
Jaridar PM News ta ruwaito cewa, Engr. Yusuf Yabagi, shugaban jam'iyyar ADP kuma kodinetan IPAC ne ya sanar da hakan a ranar Talata 26 ga watan Afrilu yayin wata liyafar buda baki da Buhari a Abuja.
Yabagi ya ce za a karrama Buhari ne saboda sanya hannu a kan dokar zabe mai dumbun tarihi domin tana wakiltar sauyi da zai tabbatar da zaman lafiya da karbuwa da zabuka a kasar.
Asali: Legit.ng