Fadar shugaba Buhari ta faɗi matakin da zata ɗauka kan duk wanda yaƙi bin umarnin Murabus

Fadar shugaba Buhari ta faɗi matakin da zata ɗauka kan duk wanda yaƙi bin umarnin Murabus

  • Fadar shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ta bayyana cewa duk wanda ya gaza yanke shawara kan umarnin murabus za'a yanke masa
  • Kakakin shugaban ƙasa, Malam Garba Shehu, ya ce sanarwan ta yi bayani dalla-dalla kan mutanen da umarnin ya shafa
  • Tuni dai wasu ministoci da ke da burin neman takara a babban zaɓen 2023 suka fara bin umarnin suka aje aikin su

Abuja - Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa duk wanda ke burin tsayawa takara kuma ya ƙi bin umarnin murabus, "zasu samu wanda zai yanke musu shawara a madadin su."

Kakakin shugaban ƙasa, Malam Garba Shehu, shi ne ya faɗi haka awanni bayan shugaba Buhari ya umarci dukkan mambobin majalisarsa da naɗe-naɗen siyasa su aje aiki idan za su yi takara.

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.
Fadar shugaba Buhari ta faɗi matakin da zata ɗauka kan duk wanda yaƙi bin umarnin Murabus Hoto: Buhari Sallau/facebook
Asali: Facebook

A jawabinsa cikin shirin 'Sunrise Daily' na Channels tv, Shehu ya ce:

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Bayan gana wa da Buhari, Wani Minista ya janye kudirinsa na takarar shugaban ƙasa

"Muna tafiyad da tsarin gwamnati, umarnin gwamnati, da sanarwan da gwamnati ta fitar ta ofishin Sakataren gwamnatin tarayya wacce shugaban ƙasa ya amince da ita. Ta yi bayani dalla-dalla kan waɗan da ake nufi."
"Saboda haka, ina tunanin a ƴan ofisoshin da umarnin ya shafa, ko ka yanke shawara da kan ka ko kuma wani daban ya yanke maka."

A cewar kakakin Buharin, sanarwar yin murabus ɗin ta yi bayani gamsasshe, inda ya jaddada cewa mutanen da abun ya shafa naɗa su aka yi.

Ministoci Tara, waɗan da ke da niyyar tsayawa takara a matakai daban-daban, ne sabon umarnin ya shafa kuma tuni wasu suka fara yin murabus.

Ƙaramin ministan ilimi ne ya fara murabus tun a wurin taron majalisar zaratarwa, daga bisani ministan kimiyya da fasaha, Mista Onu, da ministan harkokin Neja Delta, Godswill Akpabio, suka biyo baya.

Kara karanta wannan

Cikakken Labari: Wani Bam Ya Tashi a Masallaci Yayin da Mutane ke tsaka da Sallar Jumu'a

Buhari ya umarci gwamnan CBN ya aje aiki

A wani labarin kuma Bayan Ministoci, Shugaba Buhari ya umarci gwamnan CBN da wasu mutane su yi murabus

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya umarci gwamnan CBN ya yi murabus daga kujerarsa idan zai nemi takara.

Bayan umarnin ministoci, wata takarda da Sakataren gwamnati ya fitar ta tattaro dukkan masu rike da muƙamai da lamarin ya shafa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel