Da alamar NNPP za tayi wa APC taron dangi, Gawuna ya je gidan Shekarau, an ki kula shi

Da alamar NNPP za tayi wa APC taron dangi, Gawuna ya je gidan Shekarau, an ki kula shi

  • Mataimakin Gwamnan jihar Kano, Nasiru Gawuna ya je gidan Ibrahim Shekarau da nufinsu hadu
  • Haka Gawuna ya bar gidan cikin dare ba tare da ya ga Shekarau ba, alamun ya shirya barin APC
  • Tsohon Gwamnan ba zai samu takarar Sanata a APC ba, don haka ake tunanin zai iya komawa NNPP

Kano - Tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau ya ki bari su zauna da mataimakin gwamna, Nasiru Yusuf Gawuna a kan rikicin jam’iyyar APC.

Daily Nigerian ta ce Nasiru Yusuf Gawuna ya nemi ya hadu da Sanatan na Kano ta tsakiya mai-ci, Malam Ibrahim Shekarau, amma haduwarsu ba ta yiwu ba.

Hakan na zuwa ne bayan fahimtar cewa kafar Sanata Shekarau ta fara barin jam’iyyar APC mai mulki. Ana tunanin Sanatan ya gama shirin komawa NNPP.

Kara karanta wannan

Dirama a Kano yayin da tawagar Kwankwaso ta dira gidan Shekarau awanni bayan tafiyar Ganduje

Nasiru Gawuna ya shigo siyasa ne a lokacin da Shekarau yake kan kujerar gwamna a Kano. A shekarar 2003 Gawuna ya zama shugaban karamar hukuma.

Bayan Malam Shekarau ya sauka daga mulki a 2011, PDP ta karbi gwamnati. Gwamnatin Rabiu Musa Kwankwaso ta dawo da Gawuna a kujerar Kwamsihina.

Amma duk da haka mataimakin gwamnan na Kano yana ganin darajar Malam Shekarau har yau. Babu mamaki APC ta nemi tayi amfani ne da wannan alakar.

Gawuna
HE Nasiru Yusuf Gawuna Hoto: @aaibrhim1
Asali: Facebook

Zuwan Gawuna Mundubawa

Wannan ta sa ya dauki tawagar motocinsa cikin dare, ya wuce gidan Sardaunan Kano da ke Mundubawa. An yi hakan ne a daren Talatar nan da ta wuce.

Wasu tsirarun abokan siyasarsa ne suka yi wa Gawuna rakiya zuwa gidan Shekarau. Majiya ta shaidawa jaridar cewa haka suka tafi ba tare da sun hadu ba.

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Shekarau Ya Ƙi Bin Ganduje Zuwa Ganin Buhari a Abuja Bayan Gano Maƙarƙashiyar Da Aka Shirya Masa

“Da ya zo, an sanar da Malam (Shekarau) game da zuwansa (Gawuna), amma Malam ya ki yarda da su hadu da shi.”
“Daga baya sai aka shaidawa Nasiru Gawuna cewa Malam ya yi nisa a barci bayan ya sha magungunansa.” - Majiya.

Rahoton ya ce da safiyar ranar Laraba, Sanatan na Kano ta tsakiya ya hau jirgi zuwa Abuja. Alamu na kara nuna cewa bai da niyyar cigaba da zama a jam'iyyar APC.

'Yan majalisa sun koma NNPP

‘Yan Majalisar dokoki uku ne su ka yi watsi da jam’iyyar APC, duk an ji labari cewa sun sauya-sheka zuwa NNPP da Rabiu Kwankwaso ya kawo ta jihar Kano.

Sannan kuma an ji labari Nura M. Dankadai zai sauya-sheka ‘yan kwanaki kadan bayan ya yi murabus a Gwamnatin Ganduje a matsayin kwamishinan kasafi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel