A hukumance: Jita-jita ta kare, Saraki ya bayyana tsayawa takara, ya fadi dalilai
- Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, Bukola Saraki ya bayyana aniyar tsayawa takara a zaben 2023
- Saraki ya bayyana haka ne a hukumance bayan da rahotanni suka bayyana yadda shirinsa na tsayawa takara ke tafiya
- Ya zuwa yanzu, jiga-jigai daga jam'iyyun siyasar nan na ci gaba da shirye-shiryen takara a kujeru mabambanta
Bukola Saraki, tsohon shugaban majalisar dattawa ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a hukumance, TheCable ta ruwaito.
Saraki ya bayyana aniyarsa ne a wani taron karin kumallo da ‘yan jarida da wasu mukarrabansa a Abuja ranar Alhamis.
Tsohon gwamnan na jihar Kwara ya ce ya tsaya takara ne saboda akwai bukatar a magance matsalolin da suka addabi kasar nan na tsawon shekaru.
Fadar shugaban kasa ta bayyana dalilin da yasa Buhari ba zai binciki wadanda ke siyan fom din miliyan N100 ba
A kalamansa:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Dukkanmu muna da dalilan da zai sa mu damu da makomar kasar nan. Amma wannan ba lokaci ba ne na mika wuya mu kuma yanke kauna."
Maimakon cire rai da yanke kauna, Saraki ya shawarci 'yan Najeriya da su samu kwarin gwiwa tare da jajircewa wajen tabbatar da kawo sauyi Najeriya.
Da yake tabo wani bangaren rayuwarsa, Saraki ya ce:
“Na yanke shawarar zama likita domin matukar sha’awar taimako da kuma yi wa wasu hidima.
"Kuma a 1999, na shiga gwamnati a matsayin mataimaki na musamman ga shugaban kasa Olusegun Obasanjo, na kara fahimtar karin yin hidima ta hanyar gwamnati mara iyaka; da kuma yadda mulki na siyasa a hannun jagorori masu himma, cancanta da jajircewa zai iya magance matsaloli na hakika da kuma daukaka makomar kasa da al’ummarta."
Saraki ya ce idan ya zama shugaban kasa zai kara habaka kudaden shiga daga bangaren da ba na mai ba, kamar yadda Punch ta ruwaito.
A cewarsa:
“Matukar har yanzu a kasar nan akwai wadanda suke ganin za su iya karya dokokin Najeriya ba tare da wani hukunci ba; wadanda suke ganin laifin ba shi da wani sakamako, to ba a yi wani aiki ba.
"Kuma wannan shine dalilin da ya sa nake son zama shugaban kasa, saboda zan tabbatar da bin doka da oda tare da tabbatar da sakamako ga aikata laifuka."
Gwarzon Dimokradiyya: Za a karrama shugaba Buhari da babbar lambar yabo
A wani labarin kuma, nan ba da jimawa ba za a karrama shugaban kasa Muhammadu Buhari da lambar yabo ta gwarzon dimokuradiyya, wanda majalisar ba da shawara ta jam’iyyu (IPAC) za ta ba shi.
Jaridar PM News ta ruwaito cewa, Engr. Yusuf Yabagi, shugaban jam'iyyar ADP kuma kodinetan IPAC ne ya sanar da hakan a ranar Talata 26 ga watan Afrilu yayin wata liyafar buda baki da Buhari a Abuja.
Yabagi ya ce za a karrama Buhari ne saboda sanya hannu a kan dokar zabe mai dumbun tarihi domin tana wakiltar sauyi da zai tabbatar da zaman lafiya da karbuwa da zabuka a kasar.
Asali: Legit.ng