Jonathan Zai Yi Takarar Shugaban Ƙasa a 2023, Ya Yi Rajista Da APC a Mazabansa, Majiya

Jonathan Zai Yi Takarar Shugaban Ƙasa a 2023, Ya Yi Rajista Da APC a Mazabansa, Majiya

  • Wata kwakwarar majiya daga bangaren Goodluck Jonathan ta ce tsohon shugaban kasar ya yanke shawarar yin takarar shugaban kasa a 2023.
  • Majiyar ta ce tuni Jonathan ya riga ya yi rajista a jam'iyyar APC a mazabansa ta Otuoke, Jihar Bayelsa kuma zai cika fom dinsa ya mayar a wannan makon.
  • Har wa yau, majiyar ta ce Jonathan ya samu goyon bayan jiga-jigan APC, deleget da shugabannin wasu kasashen Afirka cewa ya sake yin takarar

Kimanin awa 48 bayan ya nesanta kansa da wasu kungiyoyi da suka siya masa fom din takarar shugaban kasa na 2023, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yanke shawarar fitowa takarar shugaban kasa, rahoton NAN.

A ranar 9 ga watan Mayu, Jonathan ya yi watsi da tikitin takarar da aka siya masa yana mai cewa ba da saninsa ko izininsa aka siya ba don haka bai aike su ba.

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: Wani Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a APC Ya Sake Janye Takararsa

Jonathan Zai Yi Takarar Shugaban Kasa a 2023, Ya Yi Rajista Da APC a Mazabansa, Majiya
Majiya ta tabbatar Jonathan zai yi takarar shugaban kasa a 2023, ta ce ya yi rajista da APC a mazabarsa. Hoto: Goodluck Jonathan.
Asali: UGC

An rahoto cewa ya ce cin mutunci ne wasu mutane su siya masa fom din takara ba tare da saninsa ba amma kuma yanzu tsohon shugaban kasar ya yi mi'ara koma baya kan batun.

Wata kwakwarar majiya na kusa da Jonathan, wacce ta nemi a sakaya sunanta ta ce tabbas tsohon shugaban kasar ya shiga APC, kuma ya yi rajista a mazabarsa ta Otuoke a Bayelsa.

Majiyar ta ce ana tsammanin Jonathan zai cika fom din da kungiyar fulanin suka siya masa a ya kuma mika a ranar Alhamis.

A cewar majiyar, tsohon shugaban kasar ya samu goyon bayan isasun deleget din APC daga jihohi 36 da babban birnin tarayya, Abuja.

"Jiga-jigan yan APC suma suna ta kiran Jonathan suna nuna goyon bayansu ga tsohon shugaban kasa," a cewar majiyar.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Goodluck Jonathan ba zai yi takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC ba

Wasu shugabannin Afirka sun bukaci Jonathan ya sake yin takara

Majiyar ta kuma shaidawa kamfanin dillancin labarai, NAN, a daren ranar Laraba cewa wasu shugabannin kasashen Afirka suma a ranar Litnin sun shawarci Jonathan ya sake yin takarar saboda cigaban Najeriya.

"A kalla shugbannin Afirka uku sun kira tsohon shugaban kasar kan batun, sun bukaci ya fito takarar.
"Daya cikinsu ya ce bai dace ya yi ta tafiye-tafiye yana sulhu a kasashen Afirka ba amma ya ki amsa kirar yan kasarsa.
"Wani ya gargade shi kan kin amfani da kwarewar da ya samu a matsayin tsohon shugaban Najeriya kuma dattijo," a cewar majiyar amma bata ambaci sunan shugabannin na Afirka ba.

Majiyar ta ce wasu shugabannin na Afirka sun fada wa Jonathan cewa duba da halin da kasar ke ciki, 'ana bukatar mutum wanda zai hada kan kasa kamar Jonathan.'

Jonathan Ba Zai Sake Iya Yin Takarar Shugaban Kasa Ba a 2023, Falana Ya Bada Hujja

Kara karanta wannan

Sabon salo: Birkitaccen mawaki ya fito takarar gaje Buhari a jam'iyyun siyasa har biyu

A bangare guda, Mr Femi Falana, SAN, a jiya Laraba ya ce tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ba zai iya yin takarar shugaban kasa ba a zaben 2023, Vanguard ta rahoto.

Lauya mai kare hakkin bil-adama ya ce Jonathan ba zai iya takarar ba saboda sashi na 137 (3) na kundin tsarin mulkin Najeriya ta 1999 (da aka yi wa gyaran fuska) kamar yadda SaharaReporters ta rahoto.

Ana ta hasashen cewa tsohon shugaban kasar zai iya fice wa daga jam'iyyar PDP ya koma APC gabanin zaben.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164