Sokoto: Tambuwal yayi wa gwamnatin sa garambawul

Sokoto: Tambuwal yayi wa gwamnatin sa garambawul

- Tambuwal yayi wa gwamnatin sa garambawul

- Ya nada sababbin kwamishinoni

- Ya bukaci su zage tukuru wurin yiwa al'umma aiki

Sokoto: Tambuwal yayi wa gwamnatin sa garambawul
Sokoto: Tambuwal yayi wa gwamnatin sa garambawul

Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, yayi wa wakilan gwamnatin sa garambawul, tare da kira gare su da su, dasu dinga yiwa jama'a hidima yanda ya kamata.

Mai magana da yawun bakin gwamnan, Malam Imam Imam, shine ya bayyana hakan a jiya, a wata sanarwa da yayi jiya a Sokoto.

Ya ce hudu daga cikin kwamishinonin da aka nada suna nan ba a basu ma'aikatu ba, inda tara daga cikin su aka kara sanya su a wasu ma'aikatun, saboda a kara karfafa ayyuka a jihar.

DUBA WANNAN: Janar Babangida ya kira shugaba Buhari ya bar wa yara a 2019

"Ya ce jinkirin da aka samu na bawa hudu daga cikin kwamishinonin, ya faru ne ta dalilin matsalar da aka samu da 'yan majalisun jiha akan kasafin kudi. Kowane kwamishina da shugabanin hukumomi, ya kawo tsarin kasafin kudin shi, sannan kuma majalisar wakilai, ta amince da tsarin na shekarar 2018."

Hudu daga cikin kwamishinonin da aka nada sun hada da Farfesa Aishatu Madawaki, (Minsitry of Basic and Secondary Education); Ahmad Barade Wamakko, (Social Welfare); Garba Yakubu Tsitse, (Youths and Sports); and Bello Isa Ambarura, (Commerce, Industries, Trade and Investment).

Sannan kwamishinoni tara da aka kara bawa ma'aikatu, sun hada Dokta Muhammed Jabi Kilgori, (Ministry of Higher Education); Bello Goronyo Esq, (Ministry for Energy); Musa Ausa Gidan Madi, (Ministry of Solid Minerals); and Mani Maishinku Katami, (Ministry of Rural Development).

Sauran sun hada da Abdullahi Maigwandu, (Ministry of Religious Affairs); Surajo Gatawa, (Ministry of Science and Technology); Isa Saidu Achida, (Information); Abdulkadir Jeli Abubakar, (Ministry of Home Affairs); da kuma Aminu Bello Sokoto, (Kwamishinan Ayyuka na Musamman).

Ya kara da cewar duk sauran kwamishinonin sun cigaba da rike ma'aikatun su na da.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng