Mutumin dake yanka raguna ayi shagalin dawowar Buhari daga Landan ya fice daga APC

Mutumin dake yanka raguna ayi shagalin dawowar Buhari daga Landan ya fice daga APC

  • Fitaccen masoyin shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, Alhaji Rabiu ya sauya sheka daga APC zuwa NNPP mai kayan marmari
  • Rabiu, wanda sanannen ɗan siyasa ne kuma ɗan kasuwa ya yi kaurin suna wajen yanka Raguna da shirya Fati idan Buhari ya dawo daga waje
  • Fitaccen mutumin ya kuma sayi Fom ɗin tsayawa takarar ɗan majalisa mai wakiltar Dutsin-Ma a majalisar dokokin jiha

Katsina - Ɗan a mutun shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, Alhaji Abubakar Rabiu, wanda ya shahara wajen murnan dawowar Buhari daga duba lafiya ya fice daga APC ƴa koma NNPP.

Daily Trust ta rahoto cewa Rabiu, wanda mutane suka fi sani da Abu Albarka, ya yi kaurin suna ne ta hanyar makauniyar soyayyar da yake wa shugaban ƙasa Buhari.

Kara karanta wannan

Kwankwaso da wasu manyan jiga-jigan APC sun dira filin Malam Aminu Kano

Shugaban ƙasa Buhari.
Mutumin dake yanka raguna ayi shagalin dawowar Buhari daga Landan ya fice daga APC Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Ya maida yanka raguna da shirya shagalin murnar dawowar shugaban ƙasa Buhari daga kasar waje tamkar wajibi a kansa, musamman dawowa daga ganin Likita.

Bayanai sun nuna cewa Rabiu ya yanka Raguna sau Takwas a jere domin maraba da dawowar shugaba Buhari daga wurin Likita diba lafiyarsa.

Amma a wannan Lokacin, Alhaji Rabiu wanda sanannen ɗan siyasa ne kuma ɗan kasuwa, wanda ke tare da ɗumbin magoya baya, ya bar jam'iyyar APC ya koma NNPP.

Ya kuma sayi Fom ɗin tsayawa takarar ɗan majalisar jiha mai wakiltar mazaɓar Dutsin-Ma a majalisar dokokin Katsina karkashin NNPP.

Da yake jawabi ga manema labarai jim kaɗan bayan karban Fom, Alhaji Albarka, ya ce burinsa ya bai wa mutanen mazaɓarsa gudummuwa.

Ya ƙara da bayyana cewa APC ba ta yi wani abun kirki ba don rage raɗaɗi da kyautatawa rayuwar al'ummar da suka zaɓe ta.

Kara karanta wannan

Buhari ya yi Allah wadai da kashe ɗalibar da ta zagi Annabi a Sokoto, ya nemi a yi bincike

Meyasa ya bar APC?

Wani makusancinsa da ya nemi a ɓoye bayanansa ya ce kashe burin siyasa da APC ke yi wa mabiyanta na ɗaya daga cikin dalilan da yasa Rabiu ya fice daga jam'iyyar.

Ya ce:

"APC ta rungumi yin sulhu wajen fitar da yan takara hakan na kashe kwarin guiwar wasu kuma shiyasa mutane masu burin siyasa ke ganin ba su da gurbi a jam'iyyar."

A wani labarin kuma Daruruwan mambobin APC da PDP sun sauya sheƙa zuwa jam'iyyar NNPP a Kaduna

Jam'iyyar NNPP mai kayan marmari ta ƙara karfi a jihar Kaduna yayin da take shirin tunkarar babban zaɓen 2023 da ke tafe.

Mambobin manyan jam'iyyu APC da PDP mutum 1,000 sun sauya sheka zuwa NNPP a wani yankin jihar ta Kaduna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel