Na gaji: Buhari ya ce ba zai kara kwana daya ba a karagar mulki bayan kammala 'Next Level'

Na gaji: Buhari ya ce ba zai kara kwana daya ba a karagar mulki bayan kammala 'Next Level'

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jadadda cewa zai mika mulki ga magajinsa a ranar 29 ga watan Mayun 2023
  • Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa Buhari zai mutunta kundin tsarin mulki tare da tabbatar da muradin mutane ta hanyar mika mulki ga muradinsu
  • Hakan martani ne ga kiran da babban lauyan kasar, Cif Robert Clarke, ya yi na neman shugaban kasar ya kara wa'adin mulkinsa na biyu

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce babu gudu babu ja da baya kan barinsa kujerar mulki bayan kammala wa’adin da kundin tsarin mulki ta bashi, yana mai jaddada cewa ranar 29 ga watan Mayun 2023, shine ranar da zai mika mulki ga waninsa.

Da yake magana ta hannun Malam Garba Shehu, mai magana da yawunsa, Buhari ya ce gwamnati mai ci za ta mutunta kundin tsarin mulki da kuma yancin mutane na yanke hukunci, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Mafi girman laifi ta yi: Farfesa Maqari ya goyi bayan kashe dalibar da ta zagi Annabi

Na gaji: Buhari ya ce ba zai kara kwana daya ba a karagar mulki bayan kammala 'Next Level'
Na gaji: Buhari ya ce ba zai kara kwana daya ba a karagar mulki bayan kammala 'Next Level' Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Martaninsa ya biyo bayan shawarar da Cif Robert Clarke, babban lauyan Najeriya (SAN), ya bayar cewa ya kamata a dakatar da kundin tsarin mulkin don aiwatar da sabon tsari.

Clarke ya ce shugaban kasar na iya tsawaita wa’adin mulkinsa da watanni shida idan har rashin tsaro zai iya shafar babban zaben 2023.

Dakatar da kundin tsarin mulki na iya haifar da rikici, inji Buhari

Sai dai shugaban kasar ya ce shawarar da ya bayar da bukatar dakatar da kundin tsarin mulki na iya haifar da rikici da rashin zaman lafiya.

“Da take mayar da martani ga Babban Lauyan Najeriya kan furucinsa na baya-bayan nan, fadar shugaban kasa na son bayyana kamar haka:
Cif Robert Clarke, dattijon da ake mutuntawa na iya kasancewa da gaskiya a burinsa na son a tsawaita wa’adin shugaban kasar ya kara wa'adinsa da watanni shida. Muna so mu sake nanata cewa shugaban kasa zai sauka daga mulki a ranar 29 ga watan Mayu, 2023, bayan ya kammala wa’adi na biyu – kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa ya rigamu gidan gaskiya

“Kasancewar shi ne wanda ya fara karbar mulkin dimokradiyya daga wani gwamnati mai ci a tarihin Najeriya, shugaban kasar ya himmatu wajen shimfidawa da kuma wanzar da dabi’un dimokradiyya a fadin kasar. Zai mika mulkin Najeriya ga duk wanda yan kasar suka zaba ta hanyar zabe na gaskiya da adalci."
“Sai dai, Cif Clarke ya yi daidai da ya ce idan babu tsaro, Najeriya ba za ta iya cimma hakikanin manufarta ba a matsayin kasa mai zaman lafiya da wadata. Shi ya sa wannan gwamnatin ta mayar da hankali kan haka. Sakamakon yana nan don kowa ya gani. An tilastawa yan Boko Haram ja baya daga iko da yankunan kasar nan.
“Yan gudun hijira na komawa garuruwansu don sake gina ta. An cimma wadannan nasarorin ne ta hanyar kokari da jajircewar rundunar sojojin Najeriya da jajircewar al’ummar kasarmu."

Bayan kammala 'Next Level', babban lauya ya nemi a kara wa Buhari wa’adin mulki

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: Buhari Ya Roƙi ASUU Ta Janye Yajin Aiki, Ya Ba Wa Ɗalibai Haƙuri

A baya mun ji cewa babban Lauya, kuma dattijon kasa, Cif Robert Clarke (SAN), ya yi kira da a kara wa shugaban kasa Muhammadu Buhari wa’adin mulki bayan kammala mulkinsa na biyu a 2023, Daily Trust ta ruwaito.

Babban lauyan, wanda ya bayyana hakan a ranar Litinin din da ta gabata, ya bayyana cewa watannin da ke gabanin zaben 2023 ba su isa su kawo karshen rashin tsaro ba, balle a iya zabe cikin kwanciyar hankali.

Da yake magana a gidan talabijin na Arise, Clarke ya ci gaba da cewa kundin tsarin mulkin kasar ya tanadi cewa shugaban kasa zai iya tsawaita wa’adinsa na tsawon watanni shida, tun da farko, idan yana jin cewa gudanar da zabe zai iya zuwa da tasgaro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel