‘Yan siyasan Arewa 10 baya ga Atiku, Kwankwaso, da Yarima masu harin zama Shugaban kasa

‘Yan siyasan Arewa 10 baya ga Atiku, Kwankwaso, da Yarima masu harin zama Shugaban kasa

  • Ana tunanin mulki zai bar Arewa, ya koma yankin kudu bayan cikar wa’adin Muhammadu Buhari
  • Akwai wasu ‘Yan siyasan Arewa da suke da niyyar neman kujerar shugaban kasa a zaben 2023
  • A jam’iyyar APC mutane hudu daga Arewa ne suka nuna sha’awar neman takara a zabe mai zuwa

Abuja - A rahoton nan da mu ka kawo, mun kawo sunayen wasu daga cikin wadanda suka yanki fam, suka fito neman takarar shugabanci daga Arewacin Najeriya.

Bari mu fara da ‘yan jam’iyyar PDP:

1. Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban kasar yana cikin ‘yan gaba-gaba wajen neman tikitin PDP. A zaben 2019, Wazirin Adamawa ya yi takara, amma ya sha kashi a hannun APC.

2. Bukola Saraki

Tsohon shugaban majalisar Najeriya, Bukola Saraki yana cikin wadanda za su shiga zaben fitar da gwani a PDP. Tsohon Gwamnan ya fito ne daga yankin Arewa maso tsakiya.

Kara karanta wannan

Babu abin da zai hana PDP karbe mulkin Najeriya a 2023, In ji Ayu

3. Aminu Waziru Tambuwal

Aminu Waziru Tambuwal wanda ya yi shugaban majalisar wakilan tarayyan tsakanin 2011 da 2015 zai tsaya takara kamar yadda ya yi a 2018, shi ne gwamnan Sokoto.

4. Bala Mohammed

Shi ma Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed yana cikin ‘yan gaba-gaba a zaben fitar da gwani a PDP. Tsohon Ministan zai jarraba sa’arsa a zabe mai zuwa.

Takarar Shugaban kasa
Wazirin Adamawa, Atiku Abubakar Hoto: @Atiku.org
Asali: Facebook

5. Mohammed Hayatu-Deen

Mutumin Arewa na karshe da ke takara a jam’iyyar PDP a zaben 2023 shi ne Mohammed Hayatu-Deen. Hayatu-Deen masanin harkar banki da tattali ne daga jihar Borno.

Masu neman tikitin Jam’iyyar APC

6. Ahmad Lawan

Shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan zai tsaya takara bayan an sayo masa fam a makon nan. Akwai masu ganin ya kamata 'Yan Arewa maso gabas su karbi mulki.

Kara karanta wannan

‘Yan Majalisar Kano da Kwamishinan Ganduje, za su bi Kwankwaso zuwa Jam’iyyar NNPP

7. Mohammed Badaru Abubakar

A jerin akwai Mai girma gwamnan jihar Jigawa, Mohammed Badaru Abubakar wanda ya zabi ya saye fam din zama shugaban kasa bayan an yi tunanin zai nemi Sanata.

8. Ahmed Sani Yarima

Sanata Ahmed Sani Yeriman Bakura, wanda ya yi mulki na shekaru takwas a Zamfara ya ayyana shirin takara. A zaben 2007 Bakura ya nemi zama shugaban kasa a ANPP.

9. Yahaya Bello

Tun tuni ake rade-radin Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi zai nemi shugaban kasa. ‘Dan siyasar shi ne mutumin Arewa na farko da ya yanki tikiti a jam’iyyar APC mai mulki.

Sauran Jam’iyyun hamayya

10. Rabiu Musa Kwankwaso

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya saye fam domin yin takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar adawa ta NNPP bayan ficewarsa daga PDP a karshen watan Maris.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng