2023: Kofar mu a buɗe take mu tarbi tsohon shugaban ƙasa Jonathan, Shugaban APC na Bayelsa
- Shugaban jam'iyyar APC a jihar Bayelsa, Dennis Otiotio, ya ce har yanzun tsohon shugaban ƙasa, Jonathan bai zama ɗan APC ba
- Sai dai shugaban ya ce kowane jam'iyya na da burin lashe zaɓe, dan haka kofar APC buɗe take na tarban Jonathan
- A ranar Litinin da ta gabata, wata kungiya ta saya wa tsohon shugaban Fom ɗin tsayawa takarar shugaban ƙasa a APC
Bayelsa - Shugaban jam'iyyar APC reshen jihar Bayelsa, Dakata Dennis Otiotio, ya ce tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, ya na da yancin shiga jam'iyya mai mulki amma har yanzun be sauya sheƙa ba.
Otiotio ya bayyana haka ne a wata hira da hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) ta wayar Salula, ranar Talata, 10.ga watan Mayu, 2022.
Ya kuma yi tsokaci kan yunkurin bi ta bayan fage da sanya Jonathan cikin tseren takarar shugaban ƙasa, inda ya ce APC a jihar Bayelsa ba ta da masaniyar Jonathan ya zama mamba.
Punch ta rahoto a jawabinsa ya ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Har yanzun tsohon shugaban bai yi rijitar zama mamban APC ba, yana da damar shiga duk kam'iyyar da ta kwanta masa. Kofar mu a buɗe take kuma mun shirya karban shi a jam'iyyar mu."
"A matsayin jam'iyyar siyasa da muke burin lashe zaɓe, daga cikin hanyoyin da zamu cimma nasara shi ne bai wa mutane damar shigowa cikin jam'iyya."
Kungiyar magoya baya ta saya wa Jonathan Fom
A ranar Litinin wata kungiyar magoya baya ta lale miliyan N100m da karɓi Fom na nuna sha'awa da gabatar da takara da sunan tsohon shugaban ya nemi takara karkashin inuwar APC.
Sai dai a wata sanarwar da hadiminsa, Ikechukwu Eze, ya fitar da daren Litinin, Jonathan ya nesanta kansa da batun kuma ya ce Uban Gidansa bai ba da izinin a ƙarban masa Fom ba.
A cewar Sanarwan babu wanda ya tuntuɓi Jonathan game da sayen Fom ɗin da sunansa dan haka ba shi da alaƙa da lamarin.
A wani labarin na daban kuma Majalisar Dattawa ta yi garambawul a sabon kundin zabe 2022
Majalisar Dattawa ta amince da gyara wani sashin sabon kundin zabe da zai ba zababbun shugabanni damar zama Deleget.
A kundin da shugaban ƙasa ya rattaɓa hannu a watan Fabrairu, ya hana wannan rukunin Deleget ɗin zaɓe a tarukan jam'iyyu.
Asali: Legit.ng