Da Duminsa: Majalisar Dattawa ta yi garambawul a kundin zaɓe 2022

Da Duminsa: Majalisar Dattawa ta yi garambawul a kundin zaɓe 2022

  • Majalisar Dattawa ta amince da gyara wani sashin sabon kundin zabe da zai ba zababbun shugabanni damar zama Deleget
  • A kundin da shugaban ƙasa ya rattaɓa hannu a watan Fabrairu, ya hana wannan rukunin Deleget ɗin zaɓe a tarukan jam'iyyu
  • Shugaban majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, ya ce gobe Laraba majalisar wakilai zata amince da kudirin don a kai wa Buhari

Abuja - A ranar Talata, Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da yin garambawul a kundin zaɓe 2022 domin ba Deleget masu rike da kujeru damar yin zaɓe a tarukan jam'iyyun siyasa.

Daily Trust ta rahoto cewa kundin da shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya rattafa hannu a watan Fabrairun wannan shekarar, ya hana wannan rukunin Deleget yin zaɓe a zaɓukan fidda gwani na jam'iyyu.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Bayan gana wa da Buhari, Wani Minista ya janye kudirinsa na takarar shugaban ƙasa

Zauren majalisar dattawa.
Da Duminsa: Majalisar Dattawa ta yi garambawul a kundin zaɓe 2022 Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Rukunin Deleget na zababbun shugabannin sun kunshi Kansiloli, Ciyamomin kananan hukumomi, shugabannin jam'iyya na yankuna 774, yan majalisun jiha da na tarayya.

Sauran sun haɗa da gwamnonin jihohi da mataimakansu, shugaban ƙasa da mataimakinsa, mambobin kwamitin gudanarwa na jam'iyyun siyasa, shugabannin jam'iyyu na jiha da Sakatarorin su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya zama wajibi mu yi gyaran yanzu - Lawan

Da yake jawabi bayan amince wa da kudirin, Shugaban majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, ya ce akwai bukatar gaggauta gyara sashin tun kafin fara zabukan fitar da yan takara.

Ya ce majalisar wakilai zata amince da irin wannan kudirin gobe Laraba kafin mika wa shugaban ƙasa ya rattaɓa hannu a cikin makon nan.

Lawan ya ƙara da cewa gyaran ya zama tilas domin tabbatar da babu wanda aka tauye wa haƙkinsa da ya shafi harkokin jam'iyyun siyasa, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Bayan Ministoci, Shugaba Buhari ya umarci gwamnan CBN da wasu jiga-jigan FG su yi murabus

Wannan garambawul zai ba waɗan nan Deleget dama bayan asalin Deleget da kowace jam'iyya ta zaɓa, su yi zaɓe a wurin tarukan siyasa don fitar da yan takarar kujeru daban-daban.

A wani labarin kuma Daruruwan mambobin APC da PDP sun sauya sheƙa zuwa jam'iyyar NNPP a Kaduna

Jam'iyyar NNPP mai kayan marmari ta ƙara karfi a jihar Kaduna yayin da take shirin tunkarar babban zaɓen 2023 da ke tafe.

Mambobin manyan jam'iyyu APC da PDP mutum 1,000 sun sauya sheka zuwa NNPP a wani yankin jihar ta Kaduna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel