El-Rufai, Ganduje, Umahi da Gwamnoni 8 da suka ayyana wadanda za su gaje su a 2023

El-Rufai, Ganduje, Umahi da Gwamnoni 8 da suka ayyana wadanda za su gaje su a 2023

  • Sunnar ‘yan siyasa ne, musamman Gwamnoni su ayyana wadanda za su dare kan kujera bayansu
  • Yayin da aka dumfari 2023, wasu Gwamnonin jihohin sun fadi wadanda suke sha’awar a ba tikiti
  • Akwai alamun da ke nuna wadanda aka ayyana za su yi nasarar tsayawa takara a jam’iyyun na su

Kamar yadda Legit.ng ta fitar da rahoto, jerin gwamnonin da zuwa yanzu sun shaidawa jam’iyyarsu wadanda suke goyon baya sun hada da:

1. Nasir El-Rufai (Kaduna, APC)

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya tofawa takarar Uba Sani albarka. El-Rufai ya marawa Sanatan baya ne a madadin irinsu Sani Abdullahi ‘Dattijo’.

Muhammad Sani Sha’aban, jigo a jam’iyyar APC ya nuna bai yarda da zabin gwamnan ba. Sanata tsohon abokin El-Rufai ne, ya taba zama Mai ba shi shawara.

2. David Umahi (Ebonyi, APC)

Kara karanta wannan

Takaitaccen tarihin Uba Sani wanda El-Rufai yake goyon bayan ya karbi Gwamna a 2023

An ji labari Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi ya ayyana Rt. Hon. Francis Nwifuru a matsayin wanda zai so ya yi takarar kujerar gwamna a APC a 2023.

Nwifuru shi ne shugaban majalisar dokokin jihar Ebonyi, takararsa za ta iya tada kura a APC.

3. Udom Emmanuel (Akwa Ibom, PDP)

Idan Gwamna Udom Emmanuel ya samu yadda yake so a jihar Akwa Ibom, Umo Eno ne zai rikewa jam’iyyarsa ta PDP mai mulki tuta a zabe mai zuwa.

Tun a farkon shekarar 2021, Emmanuel ya nuna karara cewa yana tare da Umo Eno. Hakan na nufin an yi waje da duk masu hangen gidan gwamnatin Uyo.

El-Rufai, Ganduje, Umahi da Gwamnoni 8 da suka ayyana wadanda za su gaje su a 2023
Gwamnonin da suka ayyana Magada Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR, David Nweze Umahi, Nasir El-Rufai, UDOM Emmanuel
Asali: Facebook

4. Samuel Ortom (Benuwai, PDP)

A wani rahoto da Punch ta fitar, ta ce Gwamna Samuel Ortom ya yi irin na Dave Umahi, yana goyon bayan shugaban majalisar jiharsa ya karbi mulki a 2023.

Kara karanta wannan

Duk mu na goyon bayan Bola Tinubu a zaben Shugaban kasa – El-Rufai ya dauki matsaya

Mataimakin gwamnan jihar Benuwai, Benson Abounu yana sha’awar zama gwamna, amma rahoton ya ce alamu na nuna Ortom na tare da Rt. Hon. Titus Uba.

5. Ifeanyi Okowa

Wani mataimakin gwamnan da yake harin darewa kujerar Ubangidansa a 2023 shi ne Kingsley Otuaro na jihar Delta, amma takararsa ta na fuskantar barazana.

Ifeanyi Okowa ya bukaci Kingsley Otuaro ya nemi kujerar Sanata domin ana zargin yana goyon bayan shugaban majalisar dokoki, Hon. Sheriff Oborevwori ne.

6. Kayode Fayemi (Ekiti, APC)

Biodun Oyebanji shi ne wanda zai rikewa jam’iyyar APC tuta a zaben sabon gwamnan jihar Ekiti da za ayi a watan Yunin 2022, ya doke sauran masu neman tutan.

Masana siyasa sun ce Mai girma Kayode Fayemi ne ya tsayawa Oyebanji a zaben tsaida gwani.

7. Okezie Ikpeazu (Abia, PDP)

A jihar Abia, ana tunanin Farfesa Uchenna Ikonne ne wanda Gwamna Okezie Ikpeazu yake so. Legit.ng Hausa ba ta da tabbacin Ikpeazu yana goyon bayansa.

Kara karanta wannan

Tauraron Mawakin Najeriya zai yi takara, Bukola Saraki ya karbe shi a Jam’iyyar PDP

8. Abdullahi Umar Ganduje (Kano, APC)

Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya nuna zai so Nasiru Yusuf Gawunan jihar Kano ya karbi kujerar Gwamna daga hannunsa a zabe mai zuwa a jam’iyyar APC.

Amma an ji labari cewa Inuwa Waya ya ce babu abin da ya dame shi da zabin da Gwamnan ya yi, ya ce hakan ba zai sa ya fasa sayen fam, ya shiga takara ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel