2023: Kotu ta ki amincewa gwamnan CBN ya tsaya takara har sai ya bar kujerarsa

2023: Kotu ta ki amincewa gwamnan CBN ya tsaya takara har sai ya bar kujerarsa

  • Kotu ta ki amincewa da bukatar gwamnan bankin CBN na tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023
  • Wannan na zuwa ne bayan da Emefiele ya shigar da AGF da hukumar zabe mai zaman kanta da zargin hana shi tsayawa takara
  • Ya ce shi ma'aikacin gwamnati ne, don haka zai iya tsayawa takara, kotu ta ce za a zauna da INEC da AGF kan lamarin ranar 12 ga wata

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ki amincewa da bukatar Gwamnan CBN, Godwin Emefiele na hana INEC da Babban Lauyan Tarayya Abubakar Malami hana shi tsayawa takarar Shugaban kasa a zaben 2023.

Gwamnan babban bankin na CBN a ranar Litinin ya shaidawa kotu a Abuja cewa zai iya tsayawa takarar shugaban kasar tarayyar Najeriya ba tare da ya bar mukaminsa na Gwamnan CBN ba.

Kara karanta wannan

Ciwon zuciya zai kama wasu: Gwamnan CBN ya ce burinsa na gaje Buhari na bashi dariya

Batun takarar Emefiele a gaban Kotu
Yanzun nan: Kotu ta ki amincewa gwamnan CBN ya tsaya takara har sai ya bar kujerarsa | Hoto: nairametrics.com
Asali: Getty Images

Gwamnan babban bankin na CBN ta bakin Lauyan sa Mike Ozekhome, ya shaida wa kotun cewa sashe na 84 ((12) na dokar zabe da aka yi wa gyara na 2022 bai shafe shi ba, kasancewarsa ma’aikacin gwamnati ne ba dan siyasa ba.

Kotu a hukuncin da ta yanke, ta gayyaci INEC, da AGF da su gurfana a gabanta a ranar 12 ga watan Mayu, don bayyana dalilin da ya sa ba za a ba Gwamnan na CBN damar tsayawa takara ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Emefiele ya roki kotun da ta bayyana shi a matsayin wanda ya cancanci tsayawa takarar shugaban kasa, kamar yadda Channels Tv ta ruwaito.

Rokon dai na daga cikin sassa bakwai da gwamnan na CBN ya gabatar a cikin karagar da ya shigar, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Tinubu ya yi magana a kan barin APC da yiwuwar samun nasara bayan rasa Jigon kamfe

Kara karanta wannan

A hukumance: Jita-jita ta kare, Saraki ya bayyana tsayawa takara, ya fadi dalilai

A wani labarin, Babban jigon APC a kudu maso yammacin Najeriya, Asiwaju Bola Tinubu ya sake jaddada cikakkiyar biyayyarsa ga jam’iyyar APC mai mulki.

Asiwaju Bola Tinubu ya nuna cewa yana nan daram-dam-dam a APC. Hakan ya sabawa rade-radin da ake yi na cewa ‘dan siyasar zai iya sauya-sheka.

A ranar Lahadi, 8 ga watan Mayu 2022, Bola Tinubu ya fito shafinsa na Twitter, ya daura hoton APC. Baya ga hoton tutan jam’iyyar APC, ‘dan siyasar a shafinsa na @OfficialBAT, ya yi wani gajeren jawabi mai matukar ma’ana, inda aka ga ya rubuta ‘100’.

Asali: Legit.ng

Online view pixel