Tinubu ya yi magana a kan barin APC da yiwuwar samun nasara bayan rasa Jigon kamfe

Tinubu ya yi magana a kan barin APC da yiwuwar samun nasara bayan rasa Jigon kamfe

  • Asiwaju Bola Tinubu bai da niyyar sauya-sheka daga jam’iyyar APC kamar yadda wasu ke tunani
  • Tsohon gwamnan na jihar Legas ya fito shafinsa na Twitter inda ya jaddada biyayyarsa ga jam’iyyarsa
  • Hakan na zuwa ne bayan Abdulmumin Jibrin ya ce zai sauya-sheka a lokacin da yake tare da Tinubu

Lagos- Babban jigon APC a kudu maso yammacin Najeriya, Asiwaju Bola Tinubu ya sake jaddada cikakkiyar biyayyarsa ga jam’iyyar APC mai mulki.

Asiwaju Bola Tinubu ya nuna cewa yana nan daram-dam-dam a APC. Hakan ya sabawa rade-radin da ake yi na cewa ‘dan siyasar zai iya sauya-sheka.

A ranar Lahadi, 8 ga watan Mayu 2022, Bola Tinubu ya fito shafinsa na Twitter, ya daura hoton APC.

Baya ga hoton tutan jam’iyyar APC, ‘dan siyasar a shafinsa na @OfficialBAT, ya yi wani gajeren jawabi mai matukar ma’ana, inda aka ga ya rubuta ‘100’.

Kara karanta wannan

‘Dan shekara 47 mai ji da kudi ya saye fam din APC, zai yi takarar Shugaban kasa a 2023

The Cable ta ce abin da hakan ke nufi shi ne tsohon gwamnan na jihar Legas yana nuna yana biyayya ga jam’iyyarsa ta APC 100 bisa 100 a zaben 2023.

Tinubu yana sallah
Bola Ahmed Tinubu Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Zan samu tikiti - Tinubu

Da ya ziyarci jihar Taraba domin ganawa da ‘ya ‘yan APC, an ji Tinubu yana cewa yana sa ran zai samu nasara wajen lashe tikitin jam’iyya na zaben 2023.

“Yiwuwar samun tikiti na yana da matukar karfi. Ina sa rai sosai. Na tabbata zan iya, kuma zan yi nasara.

The Cable ta rahoto babban ‘dan siyasar yana cewa zai fi so ayi zabe domin a tsaida gwani, a maimakon a fito da ‘dan takara ta hanyar neman maslaha.

APC: Na gaji haka nan-Hon. Jibrin

Rahoton ya ce Tinubu ya aika da wannan sako ne jim kadan bayan an ji labari Abdulmumin Jibrin ya bada sanarwar cewa ya gaji da zama a jam’iyyar APC.

Kara karanta wannan

Duk mu na goyon bayan Bola Tinubu a zaben Shugaban kasa – El-Rufai ya dauki matsaya

Hon. Jibrin yana cikin manyan magoya bayan takarar ‘dan siyasar a zaben shugaban kasa. Rade-radin sauya-shekarsa ta sa ake tunanin Tinubu ma zai bar APC.

Legit.ng Hausa ta fahimci ‘dan siyasar na Kano yana tunanin ficewa daga APC ne bayan ya fahimci wannan karo ba zai samu tikitin takarar majalisa ba.

Jibrin zai fuskanci kalubale wajen komawa majalisar wakilai daga tsohon kwamishinan Ganduje, Sanusi Sa'idu da Hon. Ali Datti Yako wanda ya doke shi a 2019.

Asali: Legit.ng

Online view pixel