Gawuna: Abubuwa 10 da ya dace Kanawa su sani kan ‘dan takarar Ganduje a zaben 2023

Gawuna: Abubuwa 10 da ya dace Kanawa su sani kan ‘dan takarar Ganduje a zaben 2023

  • Nasiru Yusuf Gawuna shi ne wanda Dr. Abdullahi Umar Ganduje yake so ya samu tikitin APC a Kano
  • Tun 2018 ne dai Mai girma Abdullahi Umar Ganduje ya dauko Gawuna a matsayin mataimakinsa
  • Kafin nan Nasiru Gawuna ya rike matsayin shugaban karamar hukuma da Kwamishina a jihar Kano

Kano - A wannan rahoto na yau, mun tattaro maku takaitaccen tarihin Nasiru Yusuf Gawuna, wanda ake tunani zai iya samun tikitin APC a jihar Kano.

Hadimin gwamnan Kano a kan kafofin sadarwa na zamani, Abubakar Aminu Ibrahim ya kawo tarihin 'dan siyasar a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi.

1. Haihuwa da tasowa

A ranar 6 ga watan Agusta 1967 aka haifi Nasiru Yusuf Gawuna a karamar hukumar nan ta Nassarawa da ke cikin birnin Kano a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Takaitaccen tarihin Uba Sani wanda El-Rufai yake goyon bayan ya karbi Gwamna a 2023

Kamar yadda Abubakar Aminu Ibrahim ya bayyana, shekarun Nasiru Gawuna kusan 55 a Duniya. Mahaifinsa, Yusuf Gawuna malamin addini ne.

Hakan ta sa ake ganin ‘dan siyasar ya tashi da ruhin addinin musulunci da sanin darajar malamai.

2. Shiga makarantar boko

Nasiru Gawuna ya fara halartar makarantar firamare ta Gawuna da ke Kano a 1973, ya samu shaidar kammala ilmin firamare a shekarar 1979.

Daga nan Gawuna ya zarce makarantar sakandaren gwamnati da ke Gwaram a 1979. A 1981 ya koma sakandaren kimiyya da ke Dawakin Kudu.

Bayan shekaru uku sai Gawuna ya samu shaidar kammala sakandare na GCE a shekarar 1984.

3. Zuwa jami’a

Tsakanin 1984 da 1985, Gawuna ya yi karatun sharan fage na IJMB a jami’ar ABU Zaria. Daga nan ya zarce zuwa jami’ar Usman Danfodio a Sokoto.

Kara karanta wannan

Kano: Tsohon Kwamishinan Ganduje Ya Fita Daga Jam'iyyar APC

Daga shekarar 1985 zuwa 1990 Gawuna ya kammala digirin BSc a fannin kimiyyar Biochemistry.

4. Fara aiki da hidimar kasa

Kamar yadda mu ka samu labari, a 1991 ne Nasiru Gawuna ya yi bautar kasa a asibitin Eastern Nigeria Medical Centre, Awkunanu da ke jihar Enugu.

Bayan nan sai Gawuna ya zama malamin zabe a hukumar zabe na NEC daga 1992 zuwa 1994.

Tun daga 1995 har zuwa 2004, Nasiru Gawuna ya yi aiki ne a karkashin hukumar da ke kula da asibitocin jihar Kano a matsayin malamin dakin gwaji.

Gawuna
Nasiru Yusuf Gawuna da Murtala Sule Garo Hoto: @aaibrhim1
Asali: Facebook

5. Shiga siyasa

A shekarar 2004 sai wannan Bawan Allah ya shiga harkar siyasa, ya kuma yi nasarar zama zababben shugaban karamar hukumarsa ta Nassarawa.

Bayan an kai ruwa rana, Gawuna ya koma kan kujerarsa ta shugaban karamar hukuma a 2007.

6. Neman takarar majalisa

Gabanin zaben 2011, Nasiru Yusuf Gawuna ya nemi zama ‘dan majalisar wakilan tarayya na yankin Nassarawa, amma bai samu tikitin jam’iyyar ANPP ba.

Kara karanta wannan

Da alamar NNPP za tayi wa APC taron dangi, Gawuna ya je gidan Shekarau, an ki kula shi

7. Zama Kwamishina

A shekarar 2013 Rabiu Musa Kwankwaso ya nada Gawuna a matsayin Kwamishinan harkar gona. Gawuna ya rike kujerarsa har bayan an canza gwamnati.

8. Mataimakin Gwamna

Da Farfesa Hafizu Abubakar ya sauka daga kujerar mataimakin gwamnan Kano a 2018, Gawuna ne wanda Abdullahi Ganduje ya zaba domin maye gurbinsa.

9. Zaben 2019

APC ba ta samu nasara sosai a yankin Kano ta tsakiya a zaben 2019 ba. Amma Gawuna yana cikin wadanda suka yi kokari wajen ganin PDP ba ta karbe mulki ba.

10. Komawa kujerarsa

Bayan an yi ta surutu kan abin da ya biyo bayan zabe, Gawuna ya cigaba da rike matsayinsa, har ya kan zama gwamnan Kano na rikon kwarya a wasu lokutan.

Gawuna zai gaji Ganduje

A jiya ne aka ji labarin yadda Gwamna Abdullahi Ganduje ya raba gardamar APC a jihar Kano, ya tsaida wanda zai gaje kujerarsa a zabe mai zuwa na 2023.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, ya karbi Fom din takara kujerar Sanata

Gwamna Ganduje ya dauki mataimakinsa watau Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin ‘Dan takarar APC tare da Murtala Sule Garo a matsayin mataimakinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel