2023: Ganduje zai yanki fam din neman takarar Sanata a APC yayin da wa’adinsa ya gabato

2023: Ganduje zai yanki fam din neman takarar Sanata a APC yayin da wa’adinsa ya gabato

  • Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya kammala shirin zama Sanatan Arewacin jihar Kano a zaben 2023
  • A ranar Litinin dinnan ake sa rai za a ji Gwamnan jihar Kano ya saye fam din shiga takara a APC
  • Watakila Gwamna Abdullahi Ganduje ya karbe kujerar da Sanata Barau Jibrin yake kai a halin yanzu

Kano - Mai girma gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya na shirin sayen fam din neman takarar ‘dan majalisar dattawa a zabe mai zuwa.

Jaridar Vanguard ta ce Dr. Abdullahi Umar Ganduje zai yanki fam da nufin ya nemi kujerar Sanatan yankin Kano ta Arewa a karkashin APC a 2023.

Gwamna Abdullahi Ganduje ya dauki wannan mataki ne bayan wani zama na musammman da ya yi da manyan masu ruwa da tsaki na APC a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ganduje Ya Dira Gidan Shekarau 'Don Ƙoƙarin Hana Shi Fita Daga APC'

Mai girma gwamnan ya sa labule da jiga-jigan jam’iyyar APC mai mulki a gidan gwamnati, idan aka tattauna kan batutuwan da suka shafi zabe mai zuwa.

Wata majiya da ta halarci taron ta shaidawa jaridar cewa a yau Litinin, 9 ga watan Mayu 2022, ake sa ran gwamnan zai biya N20m domin ya saye fam dinsa.

Legit.ng Hausa ta tabbatar da rahoton takarar gwamnan kamar yadda ta samu labari daga wajen wani daga cikin magoya bayan Sanatan da ke kan kujerar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ganduje
Gwamna Ganduje Hoto: @GovUmarGanduje
Asali: UGC

Hakan ya biyo bayan kiran da mutanensa na Dawakin Tofa suke yi da ya wakilce su a majalisa.

Ina makomar Maliya?

Idan Gwamnan ya zabi ya tafi majalisar dattawa, hakan zai jawowa Sanata Barau Jibrin babban kalubale. Tun 2015 Jibrin ne yake rike da wannan kujera.

Jibrin wanda ya fito yanki daya da Ganduje ya nuna sha’awar neman takarar gwamna a jam’iyyar APC, amma Sahelian Times ta ce bai saye fam ba tukuna.

Kara karanta wannan

Da alamar NNPP za tayi wa APC taron dangi, Gawuna ya je gidan Shekarau, an ki kula shi

Sanata Jibrin yana cikin ‘yan bangaren G7 da suke fada da bangaren Abdullahi Abbas a APC.

Tarihin kujerar Kano ta Arewa

Kafin zaben 2015 da APC ta samu nasara, Sanata Bello Hayatu Gwarzo ya shafe tsawon shekara da shekaru yana wakiltar Arewacin Kano a majalisar dattawa.

Gwarzo wanda ya yi shekaru 16 a majalisar tarayya daga 1999 zuwa 2015 shi ne ake tunanin zai zama mataimakin shugaban PDP na Arewa maso yamma.

Gwamnoni za su zama Sanatoci

Kwanakin baya mun tattaro maku jerin wasu gwamnonin da ke neman zama Sanatocin gobe. A jerin akwai gwamnonin da ke mulki a APC da kuma PDP.

Gwamnan Filato, Simon Bako Lalong shi ne gwamnan da ya fara sayen fam din Sanata. Bayan shi akwai Gwamnonin jihohin Benuwai, Delta, Enugu, da Taraba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel