A kullun Buhari na kwana da tashi da talaka a ransa – Gwamna Badaru
- Gwamnan jihar Jigawa, Abubakar Badaru, ya bayyana cewa a kullun Shugaba Buhari na kwana da tashi ne da talaka a ransa
- Badaru ya bayyana cewar shugaban kasar na mulki ne cike da tsoron Allah da kokarin ganin rayuwar talaka ya inganta
- Ya kuma zargi gwamnatin PDP da lalata kasar yana mai cewa sun tarar da ita a mace a lokacin da suka hau mulki sannan suka farfado da ita
Gwamna Abubakar Badaru na jihar Jigawa ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari na kwana da tashi da talaka a ransa.
Badaru wanda ya kasance shugaban kwamitin zaben fidda gwani na gwamnonin APC, ya bayyana hakan ne a yayin hira da Channels TV a shirin Politics Today.
Badaru ya ce:
“Shugaban kasa Buhari ya tafiyar da wannan gwamnati cikin tsoron Allah da kuma daidai iyawarsa. Kuma yana bacci da tashi da talaka a ransa; ta yaya zai inganta rayuwar talaka. Iya sanina kenan kuma saboda mutane za su ga gaskiyar abin da muke yi kuma su fahimci yanayin.
“Mun gaji mataciyyar kasa sannan muka farfado da ita. Da muka zo, jihohi 26 basa biyan albashi. Ko a lokacin suna samun kusan dala 80 kan kowace gangar mai. Yan Najeriya sun san abun da wadannan mutane suka yi kuma ba za su taba sake zabar PDP ba."
Badaru ya kara da cewa a 2023 yan Najeriya za su sake zabar APC saboda suna da tarihin abun da PDP ta yiwa kasar, Daily Trust ta rahoto.
Ya kara da cewa:
“Suna da tarihin abun da ya wakana tsakanin 1999 zuwa yau. Za su sake zabarmu saboda sun san mun jajirfce dominsu.
“Najeriya ta kasance mai tattalin arzikin da ta dogara da shigo da kayayyaki kafin zuwanmu, gaba daya ta dogara ne da mai. Kuma tunaninmu na samun kudin shiga ya ta’allaka ne a danyen mai. Muna sayar da danyen mai a kan dala 100 zuwa $140 kan kowace gangar mai kuma muna amfani da dala wajen shigo da kusan duk abin da muke amfani da shi.
“Kwatsam sai farashin ya fadi. Bukatunmu, dandanonmu da darajar kudaden shigarmu basu fadi ba, amma kudaden shiga na dala ya fadi kuma wannan tattalin arzikin da bamu tanada ba don magance abun da ke faruwa. Wani al’ajabi ne zai faru. Shin Buhari ne mutumin da ya haddasa faruwar haka?”
Kada ku barnata kuri'unku, kawai ku zabe ni – Amaechi ga wakilan APC
A wani labarin, ministan sufuri kuma mai son zama shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Rotimi Amaechi, ya ce zabarsa a matsayin wanda zai rike tutar jam’iyyar ba zai zama asarar kuri’u ba.
Amaechi ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi, 8 ga watan Mayu, a yayin da yake zantawa da wakilan jam’iyyar a jihar Edo, jaridar The Cable ta rahoto.
Ya bukaci wakilan da su mayar da hankali wajen zabar dan takarara irinsa wanda ya cancanta domin daga tutar jam’iyyar.
Asali: Legit.ng