Da duminsa: Diraktan kamfen Tinubu, AbdulMumini Jibrin, ya fita daga jam'iyyar APC

Da duminsa: Diraktan kamfen Tinubu, AbdulMumini Jibrin, ya fita daga jam'iyyar APC

  • Da alamun rikici ya sake barkewa tsakanin diraktan kamfen Tinubu da mai girma Gwamnan jihar Kano
  • Da rana tsaka, Abdulmumini Jibrin, yace ya gaji da jam'iyyar APC kuma zai koma sabuwar jam'iyya
  • Bayan alkawarin cewa ba zai sake takara kujeran majalisa ba, Jibrin ya dawo yana son yin takara

Kano - Shugaban majalisar kungiyoyin kamfen dan takaran shugaban kasa, Bola Tinubu, Hanarabul Abdulmumini Jibrin ya sanar da fitarsa daga jam'iyyar All Progressives Congress APC.

AbdulMumini Jibrin a jawabin da ya saki a shafukansa na ra'ayi da sada zumunta yace lokaci ya yi da zai hakura da APC.

Ya yi alkawarin sanar da sabuwar jam'iyyarsa nan da gobe Lahadi.

Abdul Mumin yace:

"Na yiwa APC iyakan kokari na. Zan sanar da sabuwar jam'iyyata nan da sa'o'i 24 Insha Allah. Bayan hakan zan saki jawabi na musamman."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ministan Buhari Da Ya Yi Murabus Don Takarar Gwamna Ya Janye Takararsa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Abdulmumini Jibrin ya fadi ba nauyi, Ali Datti ya lashe zaben

Zaku tuna cewa dan majalisan wakilan tarayya, AbdulMumini Jibrin, ya fadi ba nauyi a zaben mai-mai da aka gudanar a mazabar Kiru/Bebeji na jihar Kano.

Jibrin wanda yake dan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya sha kasa hannun abokin hamayyarsa Alhaji Ali Datti Yako, na Peoples Democratic Party (PDP) da aka gudanar 25 ga Junairu, 2020.

Baturen zaben, Farfesa Abdullahi Arabi, ya ce Ali Datti ya samu kuri'u 48,641 yayinda AbdulMumini Jibrin ya samu kuri'u 13,507.

Kafin faduwarsa wannan karon, Abdul Mumini Jibrin ya kasance a majalisar wakilai tun shekarar 2011 a matsayin dan PDP amma daga baya ya sheka APC.

Gabanin zaben nan, dan siyasan ya shiga takun saka da shugabannin jam'iyyarsa a jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel