Rikicin PDP a Kano: Makusantan Sanata Kwankwaso uku sun shiga komar yan sanda, An fallasa sunayen su
- Wasu mabiya tsagin Kwankwasiyya na jam'iyyar PDP sun shiga hannun hukumar yan sanda a Kano
- Kakakin yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce ana zargin mutunen uku ne da kai wa yan ɗaya tsagin PDP hari
- Shugaban PDP na Kano, Shehu Wada Sagagi, ya bayyana yadda rikicin ya faru a Otal ɗin Tahir Guest Palace
Kano - Rundunar yan sanda reshen jihar Kano ta yi ram da wasu mutum uku magoya bayan tsagin tsohon gwamna, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, a jam'iyyar da ya fice wato PDP.
Kwankwaso ya fice daga PDP ya koma jam'iyyar NNPP mai kayan marmari a ƙarshen watan Maris, sai dai har yau tsaginsa a PDP ne ke jan ragama karkashin Alhaji Shehu Wada Sagagi.
Kano: Shugaban Ma'aikatan Fadar Ganduje, Shugaban Karamar Hukuma, Ƴan Majalisa 2, Auditan APC Da Shugaban Matasa Duk Sun Koma NNPP
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa an kama mutum ukun ne kan harin baya-bayan nan da aka kai wa mutum 5 na ɗayan tsagin jam'iyyar PDP.
Da yake bayyana sunayen mutanen a Kano ranar Alhamis, kakakin rundunar yan sandan, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce an kame Malam Dahiru Haruna, Msta Idi Zare Rogo, da kuma Idris Yau Mariri.
Ya ƙara da cewa dakarun yan sanda na tsare da mutane a hedkwatar hukumar yan sanda da ke Bompai.
Kiyawa ya ce sun damƙe mutum uku ne bisa bibiya har zuwa ɗakin Otal ɗin waɗan da suka kawo ƙara, suka farmake su kuma suka ci mutuncin su.
Ya ce an cafke mutanen ne yayin da suka farmakin bangaren PDP kuma daga baya aka tabbatar yan tsagin Kwankwasiyya ne.
Rikicin da ya faru
Wani rikici ya ɓarƙe ranar Laraba da yamma tsakanin shugabannin PDP na Kano da kuma wakilan uwar jam'iyya ta ƙasa.
Rahoto ya nuna cewa rikicin ya faru ne a Otal ɗin Tahir Guest Palace wurin da aka sauki ɗaya daga cikin wakilan hedkwatar jam'iyya ta ƙasa.
Shugaban PDP a Kano, Shehu Sagagi, ya ce bayan tarban wakilin a Filin jirgin Malam Aminu Kano kuma aka kai shi Otal ɗin, ya nemi a kawo masa abin sha.
"Lokacin da suka dawo kawo masa abin sha sai suka taras baya nan, amma sun bibiyi inda ya shiga zuwa ɗaki mai lamba 811, nan rikicin ya fara," inji shi.
A wani labarin na daban kuma Kotu ta ɗaure tsohon babban hadimin gwamnati shekara 12 a gida Yari
Kotun tarayya dake zamanta Legas ta yanke wa tsohon sakataren Dindindin a ma'aikatar kwadugo hukuncin shekara 12 a Yari.
Kotun ta tabbatar da laifin da ake tuhumarsa ne bayan ya canza shaidarsa ya amsa laifinsa bayan da farko ya musanta.
Asali: Legit.ng