Da Dumi-Dumi: Kotu ta ɗaure tsohon Sakataren Dindindin shekara 12 a gidan yari

Da Dumi-Dumi: Kotu ta ɗaure tsohon Sakataren Dindindin shekara 12 a gidan yari

  • Kotun tarayya dake zamanta Legas ta yanke wa tsohon sakataren Dindindin a ma'aikatar kwadugo hukuncin shekara 12 a Yari
  • Kotun ta tabbatar da laifin da ake tuhumarsa ne bayan ya canza shaidarsa ya amsa laifinsa bayan da farko ya musanta
  • Hukumar EFCC ta gurfanar da tsohon sakataren gaban Kotu ne bisa tuhume-tuhume uku

Lagos - Babbar Kotun tarayya dake zama a jihar Legas, a ranar Alhamis ta ɗaure tsohon Sakataren dindindin na ma'aikatar kwadugo, Dakta Clement Illoh, bisa ƙin bayyana dukiyarsa.

Alƙalin Kotun mai shari'a Babs Kuewunmi, ya yanke wa Mista Illoh hukuncin, wanda ya amsa laifinsa bayan da farko ya musanta, tsawon shekara hudu a gidan Yari bayan masu gabatar da ƙara sun gama aikin su.

Tsohon Sakataren Dindindin, Clement Illoh.
Da Dumi-Dumi: Kotu ta ɗaure tsohon Sakataren Dindindin shekara 12 a gidan yari Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

A rahoton Daily Trust Alƙalin ya ce:

Kara karanta wannan

Cikakken Labari: Wani Bam Ya Tashi a Masallaci Yayin da Mutane ke tsaka da Sallar Jumu'a

"Na maida hankali na yi nazari matuka kan jawabin wanda ake ƙara, duk da haka Kotu ba zata fasa gabatar da aikinta ba bisa tanadin doka."
"Saboda haka, ina mai sanar da yanke wa wanda ake ƙara hukuncin zaman Yari na shekara hudu a kowane tuhuma da ake masa kuma zai fara tun daga ranar 10 ga watan Oktoba, 2019."

Bayan haka alƙalin ya ba da umarnin kwace makudan kuɗi naira N97,300,613.44, Dala $139,575.50 (Kusan miliyan N58m) da kuma dala £10,121.52 (kimanin N4,453,000) daga hannun shi a baiwa FG.

Tuhuma nawa ake zargin Mista Illoh da su?

Hukumar yaƙi da yi wa tattalin arzikin ƙasa ta'adi (EFCC) ta gurfanar da tsohon hadimin gwamnatin tarayya ne bisa tuhume-tuhume guda uku, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari ya faɗi matakin da gwamnatinsa zata ɗauka kan duk ɗan takarar da yaƙi yin murabus

Tuhuma ta farko, Kotu ta ji cewa wanda ake ƙara a ranar 19 ga watan Afrilu 2019, ya gaza bayyana ainihin yawan kadarorin da ya mallaka da suka kai miliyan N97.3m wanda hakan ya saɓa wa tanadin doka.

Tuhuma ta biyu, ya gaza bayyana dukiyarsa da ta kai dala dubu $139,575, yayin da a tuhuma ta uku ya ɓoye mallakar £10,121.

A ranar Alhamis ya yi amai ya lashe bayan tafka muhawara da lauyan EFCC, Rotimi Oyedepo, wanda ya bayyana cewa wanda ake zargi ya karɓi miliyan N65m daga ɗan kwangilan Sure-p ta asusun sa na kai da kai.

Yayin haka ne lauyan wanda ake ƙara, Mr T.S. Awana, ya nemi izinin Kotu na tattauna wa da wanda yake karewa, biyo bayan haka ne ya canza shaidarsa a gaban Kotu.

Bayan haka ne, Kotu ta kama shi da aikata laifukan kuma ta yanke masa zaman gidan ƙaso na shekara hudu a kowace tuhuma ɗaya, jimulla shekara 12 kenan.

Kara karanta wannan

Bayan Ministoci, Shugaba Buhari ya umarci gwamnan CBN da wasu jiga-jigan FG su yi murabus

A wani labarin na daban kuma Magidanci ya lakaɗa wa matarsa dukan tsiya, ya yi barazanar kasheta kan ta cika kwalliya 'Make-Up'

Yan sanda a Legas sun gurfanar da wani Magidanci gaban Kotu kan zargin barazanar kashe matarsa.

Ana tuhumar Magidancin da lakaɗawa matarsa dukan tsiya da kuma faɗa mata zai ga bayanta kan yawan amfani da Make-Up.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262