2023: Kungiyoyi 102 Sunyi Karo-Karo Sun Haɗa N50m Don Siya Wa Gwamnan Zamfara Fom Ɗin Takara
- Wasu kungiyoyi guda 102 a Jihar Zamfara sun yi karo-karo sun siya wa Gwamna Bello Matawalle fom din takara a 2023
- Yusuf Idris, mai magana da yawun jam'iyyar APC a jihar Zamfara ya ce kungiyoyin sun yi wannan karamcin ne don sun gamsu da irin salon mulkin Matawalle
- Idris ya ce a yau Juma'a ne za a yi taron gabatar da kudin fom din ga Gwamnan na Zamfara bayan Sallar Juma'a inda za a yi tattaki zuwa gidan gwamnati
Zamfara - Jam'iyyar APC, a ranar Alhamis, a Jihar Zamfara, ta sanar da mika takardar kudi 'cheque' na Naira miliyan 50 domin siya wa Gwamna Bello Matawalle fom din sake takarar gwamna a jihar, rahoton NAN.
Mai magana da yawun jam'iyyar APC, Yusuf Idris, ya yi ikirarin kungiyoyi 102 a jihar ne suka hada kudi domin siya wa gwamnan fom din takarar, rahoton Premium Times.
Ya ce za a yi taron gabatar da kudin a hukumance a ranar Juma'a daga nan magoya bayan gwamnan za su yi tattaki daga filin Idi na Gusau zuwa gidan gwamnati inda za a mika wa gwamnan cheque din.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Bisa gamsuwa da amanna da salon mulkin Gwamna Bello Matawalle, kungiyoyin sun tara Naira miliyan 50 da nufin tallafawa gwamnan siyan fom din takarar kujerar gwamna a APC a zaben 2023.
"Don haka ne, jam'iyyar APC a jihar ke gayyatar dukkan mambobi, magoya baya da masoya zuwa taron mika cheque din na N50m ga gwamnan," in ji Idris.
Ya kara da cewa shugaban jam'iyyar APC na jihar, Tukur Danfulani ne zai gabatar da cheque din ga gwamnan.
"Shugaban jam'iyyar a jihar ya mika godiyarsa ga kungiyoyin 102 da magoya baya bisa wannan karamcin yana mai tabbatar musu cewa APC ba za ta basu kunya ba," in ji Mr Idris.
'Abokan Tambuwal' Sun Siya Masa Fom Takarar Shugabancin Ƙasa
A bangare guda, wata kungiya mai suna Abokan Tambuwal sun siya wa gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal fom din takarar zaben shugaban kasa a jam'iyyar PDP.
Kungiyar, karkashin jagorancin Aree Akinboro, sun siya fom din ne a ranar Alhamis a hedkwatar jam'iyyar da ke birnin tarayya Abuja, The Cable ruwaito.
PDP ta tsayar da ranar 28 ga watan Mayu domin zaben yan takarar da za su wakilci jam'iyyar a zaben na 2023.
Asali: Legit.ng