‘Danuwan mai neman takarar Shugaban kasa ya fice daga APC, ya kafa sabuwar jam’iyya

‘Danuwan mai neman takarar Shugaban kasa ya fice daga APC, ya kafa sabuwar jam’iyya

  • Sanata Orji Uzor Kalu ya yi magana a game da wani ‘danuwansa da ya fice daga jam’iyyarsu ta APC
  • Tsohon Gwamnan Abia ya ce manya sun roki Mascot Uzor Kalu ya zauna a APC, amma ya ki yarda
  • Orji Uzor Kalu bai da labarin Mascot Kalu ya sauya-sheka har ta kai ya kafa wata sabuwar jam’iyya

Abuja - Mascot Uzor Kalu, wanda kani ne ga Sanata Orji Uzor Kalu ya yi watsi da jam’iyyar APC mai mulki, ya kafa wata sabuwar jam’iyya a Najeriya.

Punch ta ce jam’iyyar da Mascot Uzor Kalu ya kirkiro ita ce Action Peoples Party watau APP.

Da yake bayani a shafinsa na Facebook, Orji Uzor Kalu ya ce an yi kokarin a hana Mascot Uzor Kalu barin APC, amma ya ki sauraron masu wannan kira.

Kara karanta wannan

Tauraron Mawakin Najeriya zai yi takara, Bukola Saraki ya karbe shi a Jam’iyyar PDP

Kamar yadda tsohon gwamnan na Abia ya shaida a shafinsa, shugabannin jam’iyyar APC sun yi zama da ‘danuwansa, amma duk aka gaza shawo kansa.

Jawabin Mascot Uzor Kalu a Facebook

“Na samu kira da-dama daga aminai, abokan siyasa, masu ta-cewa a harkar siyasa da jagororin al’umma domin jin ra’ayi na kan sauya-shekar ‘danuwana, Mascot daga APC zuwa APP.”
“Maganar gaskiya, shugaban jam’iyya na kasa, mataimakan shugabannin jam’iyya biyu na APC, har da shugaban majalisar dattawa sun lallabe shi ya zauna a APC, amma sai ya ki yarda.”
Sanatan Abia
Orji Uzor Kalu Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Abin da ban mamaki

“Na yi mamakin jin cewa shi da wasu masu ta-cewa a harkar siyasa sun kafa sabuwar jam’iyya, Action Peoples Party, APP, a jiya (Laraba) a garin Umuahia ba tare da an sanar da ni ba.”

Kara karanta wannan

Saraki ya bada labarin zamansa Shugaban Majalisa a 2015 duk da adawar Bola Tinubu a APC

“To, ba ni da wata matsala da ‘danuwana, yana da damar da zai dauki mataki game da siyasarsa, kuma a matsayina na mai bin tsarin damukaradiyya, na san da haka, ina masa fatan alheri.”

Ina nan a APC - Kalu

Daily Post ta ce a karshe Sanatan na Arewacin jihar Abia ya karkare zancensa da cewa har gobe yana rike da mukaminsa a majalisa, kuma yana tare da APC.

Bugu da kari, Uzor Kalu ya ce zai cigaba da kokarin kawowa mazabarsa romon damukaradiyya.

Mascot Kalu ya rike kujerar shugaban ma’aikatan tsohon gwamnan, kuma ya yi takarar kujerar Aba ta Kudu/Arewa a majalisar wakilan kasa a karkashin APC.

Ban ci amanar Tinubu ba - Fayemi

Dazu aka ji Gwamnan jihar Ekiti ya yi karin-haske a kan takarar shugabancin Najeriya da yake yi a APC, duk da tsohon mai gidansa ya na neman tuta a jam'iyya.

Dr. Kayode Fayemi ya ce neman tikitin jam’iyyar APC ba yunkurin juyawa Bola Tinubu baya ba ne. A cewar gwamnan kujerar shugaban kasa ba gadon wani ba ne.

Kara karanta wannan

Guguwar NNPP na neman ratsa siyasar Kano, Shekarau da su Sumaila za su fice daga APC

Asali: Legit.ng

Online view pixel