Dalilin da yasa na cancanci zama shugaban ƙasa a Najeriya, Oshiomhole

Dalilin da yasa na cancanci zama shugaban ƙasa a Najeriya, Oshiomhole

  • Tsohon shugaban APC na ƙasa, Adams Oshiomhole, ya ce tulin kwarewar da ya samu ta isa a ba shi dama ya gaji Buhari a 2023
  • Oshiomhole, wanda ya ayyana tsayawa takarar Sanata, ya ce ya gano cewa kujerar shugaban ƙasa ce ta dace da shi a Najeriya
  • Ya kuma yi bayanin yadda za'a kawo ƙarshen yajin aikin kungiyar Malaman jami'o'i ta ƙasa ASUU

Abuja - Tsohon shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Kwamaret Adams Oshiomhole, ya bayyana dalilin da yasa ya cancanci a zaɓe shi shugaban kasa a 2023 a Najeriya.

Tsohon gwamnan jihar Edo ya ce yana da kwarewa a fannoni daban-daban na rayuwa, da suka haɗa da ƙungiyanci da hukumomi masu ƙalubale, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Kwamaret Oshiomhole ya yi wannan jawabin ne a shirin Labaran Arise ranar Laraba lokacin da yake tsokaci kan nufinsa na tsayawa takarar shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Bayan gana wa da Buhari, Wani Minista ya janye kudirinsa na takarar shugaban ƙasa

Kwamaret Adams Oshiomhole.
Dalilin da yasa na cancanci zama shugaban ƙasa a Najeriya, Oshiomhole Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Tsohon shugaban jam'iyya mai mulkin ya ce:

"Idan kuka duba tushe na, na tsallake kowane irin siraɗi, na yi aiki a karamin mataki, na kai kololuwa a ma'aikata, an jarabce ni da mulki a tattalin arziki, muƙamin siyasa, na yaƙi masu mulki da bincike su."
"Bayan haka na zama gwamnan jihar Edo inda na yi koƙarin aiwatar da wasu abubuwa da na jima ina faɗa lokacin ina ƙungiyar Kwadugo NLC."

Yadda zan shawo kan matsaloli kamar na ASUU - Oshiomhole

Bayan haka tsohon shugaban ƙungiyar kwadugon ya bayyana hanyar da zai kawo ƙarshen yajin aikin ASUU da zaran ya zama shugaban ƙasa.

Ya ce malaman jami'o'i sun shiga yanayin rashin kuɗaɗen shiga dan haka akwai buƙatar kyautata musu albashi.

Ya ce:

"Idan Farfesa yana ɗaukar N500,000 wanda ke bi masa me shirin zama Farfesa yana ɗaukar N300,000, babban Lakcara yana ɗaukar wataƙila N200,000, me kuke tsammani?"

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Ɗiyar tsohon ministan Abuja da wasu mutum 11 sun mutu a hatsarin jirgin sama

"Abun da na fahimta a rayuwa tun ina gwamna shi ne abun da kake samu ba shi zai nuna ayyukan da zaka yi ba. ASUU wani ɓangare ne na yan Najeriya kuma abun da suke bukata mai sauki ne."

A wani labarin na daban kuma Gwamnan APC a Arewa da wani Ministan Buhari sun ayyana tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2023

Gwamnan jihar Jigawa a arewacin Najeriya, Abubakar Badaru, ya sayi Fom din tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2023.

Ministan harkokin Neja Delta, Godswill Akpabio, ya bi sahun gwamnan ya tara masoya ya bayyana kudirinsa idan ya zama shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel