2023: Najeriya na bukatar mahaucin mutum da zai dawo da komai kan hanya, Gwamna Wike
- Gwamna Wike na jihar Ribas kuma ɗan takarar shugaban kasa ya ce akwai bukatar Najeriya ta samu mahaukacin shugaba a 2023
- Acewar gwamnan ta haka ne kaɗai za'a iya dawo da komai kan turbar cigaba kuma ya shirya yi wa ƙasa aiki da karfinsa
- A ziyarar da ya kai don neman kuri'un Deleget na PDP a Kogi, Wike ba zai iya fita daga cikin jam'iyga ba don an hana shi takara
Kogi - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya ce yanayin Najeriya ya yi muni ta yadda a yanzu ƙasar na bukatar mahaukaci wanda zai dawo da komai kan hanya don gyara.
Gwamnan, ɗan takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin PDP ya yi wannan furucin ne yayin da yake jawabi ga Deleget na jam'iyya a jahar Kogi ranar Laraba, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Wike ya roki Deleget ɗin su kaɗa masa kuri'un su a zaɓen fidda gwanin PDP, inda ya ce yana da duk abin da ake bukata na jan ragamar Najeriya zuwa matakin cigaba.
Gwamnan ya ce:
"Kuzaharin da ke tattare da ni ya yi yawa, ina son amfani da shi wajen yi wa ƙasata hidima. Na shirya kaina a jam'iyya da kuma cin nasara har na zama shugaban tarayyan Najeriya."
"A tarihin Najeriya ba mu taɓa rabuwa ba, zan iya dawo da ƙasar nan kan turbar da ta bari na girma, yankin da mutum ya fito ba abun dubawa bane, ana bukatar mahaukaci ya jagoranci Najeriya."
Ana bukatar shugaba mara tsoro - Wike
Wike ya ƙara da cewa Najeriya na bukatar mara tsoro kuma me kwarin guiwa da kwarjini kamar shi, wanda zai faɗi gaskiya ga masu rike da madafun iko.
"A bangarena, idan baku zaɓe ni ba, ba zan fita daga PDP ba, zan cigaba da zama mamba domin na amfana da jam'iyya, saboda haka ban da uzurin da zai jawo na koma wata jam'iyya."
A wani labarin kuma Ɗan takarar Shugaban ƙasa, Rotimi Amaechi, ya zargi wani rukumin manyan mutane da jefa Najeriya cikin matsaloli
Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya ɗora laifin matsalolin da Najeriya ke ciki a wuyan manyan mutane masu mukamai.
Ɗan takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin inuwar APC ya buƙaci ƴan Najeriya su fara tuhumar yan siyasa kan harkokin shugabancin da suka tura su.
Asali: Legit.ng