Mutane masu matsayi ne suka jefa Najeriya cikin matsaloli, Rotimi Amaechi

Mutane masu matsayi ne suka jefa Najeriya cikin matsaloli, Rotimi Amaechi

  • Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya ɗora laifin matsalolin da Najeriya ke ciki a wuyan manyan mutane masu mukamai
  • Ɗan takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin inuwar APC ya buƙaci ƴan Najeriya su fara tuhumar yan siyasa kan harkokin shugabancin da suka tura su
  • A cewarsa har sai lokacin da mutane suka farka daga bacci suka fara bibiyar amanar da suka ba yan siyasa, kasar nan ba zata cigaba ba

Akwa Ibom - Ministan Sufuri, kuma ɗan takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin APC, Mista Rotimi Amaechi, ya zargi manyan masu matsayi da ƙara jefa kasar nan cikin ƙaƙanikayi.

Daily Trust ya rahoto cewa Amaechi ya yi wannan zargin ne a wurin taron 'ranar yancin yan jarida ta duniya' wanda ƙungiyar yan jarida ta ƙasa (NUJ) ta shirya a Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom.

Kara karanta wannan

Dalibai mata na jami'o'i biyu a Arewa zasu fito tituna zanga-zanga tsirara kan yajin aikin ASUU

Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi.
Mutane masu matsayi ne suka jefa Najeriya cikin matsaloli, Rotimi Amaechi Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Ministan ya ce:

"Matsalar Najeriya ba talakan Akwa Ibom ko na Ribas bane ya jawo, ba talakan kudu maso gabas bane ko na yankin Arewa. Ni da kai ne matsalar, masu matsayi."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ku tuhumi yan siyasa - Amaechi ga yan Najeriya

Ministan ya kuma ƙalubalanci yan Najeriya su tuhumi yan siyasa su riƙa musu bayani dalla-dalla kan ayyukan su na shugabancin da suka tura su.

Amaechi, wanda ya kasance babban baƙo a wurin taron, ya ce:

"Har sai lokacin da muka fara rike kowane dan siyasa, kowane mai rike da wani matsayi ya mana bayani, ƙasar nan ba zata taɓa cigaba ba."

A cewar Minsistan, masu rike da muƙamai suna ta ɓaɓatun a sake fasalin ƙasa ne saboda sun gano babu sauran abubuwan da zasu ƙasafta tsakanin su.

"Dalilin da yasa muka koma jin a sake fasali a sake fasalin ƙasar na shi ne saboda shugabanni sun fara ganin cewa mun talauce arzikin ya fara dusashewa, ba bu kuɗin karkatarwa."

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Bayan gana wa da Buhari, Wani Minista ya janye kudirinsa na takarar shugaban ƙasa

"Matsalar da Najeriya ke fuskanta duk manyan masu rike da muƙamai ne suka jawo mana shi, ciki har da kai."
Bugu da ƙari Ministan ya roki yan jarida da su tallafawa ƙoƙarin da ake na gano hanyoyin warware matsalolin ƙasar nan, inda ya ce: "Yanci na zuwa ne tare da haƙƙoƙi da nauyi."

A wani labarin na daban kuma Shugaba Buhari ya ce ba ya iya bacci da daddare saboda matsalar tsaron Najeriya

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya ce ko kaɗan ba ya iya kwantawa ya yi bacci saboda matsalar tsaron da ta dami Najeriya.

Jim kaɗan bayan kammala Sallar Idi a Barikin Mambila, Buhari ya ce ba zai raga wa yan ta'adda ba har sai ya ga bayan su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel