2023: 'Yan APC a yankin Yarbawa za su zauna, su hada kai su zabi mai gaje Buhari daga yankinsu

2023: 'Yan APC a yankin Yarbawa za su zauna, su hada kai su zabi mai gaje Buhari daga yankinsu

  • Rahotanni da ke fitowa a yankin Kudu maso Yamma na nuni da cewa, jiga-jigan yankin za su yi amfani da ikonsu wajen hade kan 'yan APC
  • Manufar hada kai da taron da za su yi shi ne a samar daya kwakkwara daga yankin wanda APC za ta ba tikitin takara na 2023
  • Sai dai, kusan dukkan yankunan kasar nan na ci gaba da nuna sha'awar samar da dan takara tilo a zaben mai zuwa

Jihar Legas - Shugabanin jam’iyyar APC na yankin Kudu maso Yamma za su gana da masu neman takarar shugaban kasa na yankin a ranar Juma’a a jihar Legas, kamar yadda jaridar WesternPost ta ruwaito.

An bayyana cewa taron zai gudana ne a gidan gwamnatin Legas.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Hadimin Buhari, Bashir Ahmad ya yi murabus daga kujerarsa

Rahoton da Legit.ng Hausa ke samu daga TheCable ya bayyana cewa Bisi Akande, tsohon shugaban riko na jam’iyyar APC ne zai jagoranci taron.

Yadda Yarbawa za su samar da tikitin takarar APC daga yankinsu
2023: 'Yan APC a Kudu maso Yamma za su hada kai su zabi mai gaje Buhari daga yankinsu | Hoto: researchgate.net

An ce shugabannin yankin sun damu matuka da yawan masu neman tikitin jam’iyyar APC daga yankin Kudu a zaben 2023 mai zuwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wadanda aka gayyata taron dai sun hada da kakakin majalisar wakilai Femi Gbajabiamila da gwamnonin jam’iyyar APC na shiyyar da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Farfesa Ajayi Boroffice da sauran shugabannin APC na shiyyar, inji Daily Trust.

Makasudin taron manyan yankin Yarbawa

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, Bola Tinubu, tsohon gwamnan Legas; Kayode Fayemi; Gwamnan Ekiti; da Ibikunle Amosun, tsohon gwamnan Ogun, na daga cikin ‘yan takarar shugaban kasa daga yankin Kudu maso Yamma.

Makasudin taron dai shi ne a fitar da tsare-tsare don ganin cewa yankin Kudu maso Yamma bai rasa tikitin takarar ba saboda yawan masu fatan gaje Buhari da suka bayyana sha’awarsu ta tsayawa takara, kamar yadda aka bayyana.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Gwamnonin PDP sun shirya ganawar gaggawa gabanin zaben fidda gwani

Majiya ta bayyana cewa:

“Akande, wanda ake mutuntawa a duk bangarorin siyasar a yankin, da sauran wadanda suka kira taron suna son ganin an rage jerin sunayen ‘yan takarar Kudu maso Yamma domin kada yankin ya rasa tikitin takarar shugaban kasa na APC.”
“Shugabannin sun damu cewa idan yankin Kudu maso Yamma bai samu hadin kai ba, muna iya rasa tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC zuwa wani yanki. Abu ne da ya fi daukar hankali a ce ‘yan jam’iyyar APC guda hudu ‘yan inuwar siyasa daya ne.
“Kudu-maso-Gabas na yin mai yiwuwar tsayar da dan takarar shugaban kasa. Hatta Kudu-maso-Kudu da suka yi Shugaban kasa da a baya-bayan nan; Shugaba Jonathan, suna son a sake basu dama ganin 'yan takara na fitowa daga yankin.”

A halin da ake ciki dai, jam’iyyar APC ba ta dau wani mataki a hukumance ba kan batun inda za ta mika tikitin takarar shugaban kasa na zaben 2023 mai zuwa ba, amma na ci gaba da kai ruwa rana.

Kara karanta wannan

2023: Bafarawa da wasu mutum 4 da su ka hakura da neman Shugaban kasa da dalilansu

Shugaban kasa a 2023: Jerin sunayen wadan da suka sayi Fom da masu shirin saye kan Miliyan N100m a APC

A wnai labarin, yayin da wa'adin sayar da Fom na APC ke gab da ƙarewa, shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, fitaccen ɗan kasuwa, Gbenga Olawepo-Hashim, na shirin lale N100m su sayi Fom ɗin takarar shugaban kasa.

Daily Trust ta ce zuwa yanzun yan takara Shida sun karbi Fom bayan biyan N100m, sun haɗa da, Bola Tinubu, Gwamna Yahaya Bello na Kogi da gwamna Dave Umahi na Ebonyi.

Sauran sune; ƙaramin ministan Ilimi, Emeka Nwajiuba, Sanata Rochas Okorocha, sai kuma yar takara mace, Uju Kennedy, wacce ta karbi Fom ɗin bayan biyan N30m bisa umarnin APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel