2023: Kawunan sanatocin APC ya rabu kan yunkurin tsayar da Lawan a matsayin dan takarar maslaha

2023: Kawunan sanatocin APC ya rabu kan yunkurin tsayar da Lawan a matsayin dan takarar maslaha

  • Ga dukkan alamu, shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan na iya bayyana a matsayin dan takarar maslaha na majalisar dokokin tarayya
  • An tattaro cewa wasu tawaga a majalisar dattawan suna ta kokarin ganin Lawan ya zama dan takarar
  • Majiyoyi na kusa da shi sun bayyana cewa zai shiga tseren shugabancin kasar a wannan makon

Abuja - Rahotanni sun kawo cewa baraka ya kunno kai a tsakanin sanatocin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) kan kokarin da ake na tsayar da shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan a matsayin dan takarar shugaban kasa na maslaha.

Lawan, wanda ke majalisar dokokin kasar tun 1999, na shirin ayyana kudirinsa na takarar shugaban kasa a wannan makon, kamar yadda majiyoyi na kusa da shi suka bayyana.

Sai dai shugaban majalisar dattawan ya fadama yan jarida cewa Allah ne kadai zai zartar da hukunci a kan mataki na gaba da zai dauka a lokacin da aka tambaye shi game da shirin da wasu manya ke yi a arewa don mara masa baya ya zama shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Sabon salo: Birkitaccen mawaki ya fito takarar gaje Buhari a jam'iyyun siyasa har biyu

2023: Kawunan sanatocin APC ya rabu kan yunkurin tsayar da Lawan a matsayin dan takarar shugaban kasa
2023: Kawunan sanatocin APC ya rabu kan yunkurin tsayar da Lawan a matsayin dan takarar shugaban kasa Hoto: @NGRSenate
Asali: Twitter

Daily Trust ta tattaro cewa gabannin ayyana kudirin nasa na son shiga takarar, ana shirin gabatar da shi a matsayin dan takarar maslaha na majalisar dattawan.

An tattaro cewa wasu makusantansa a majalisar da suka hada da Sanata Yusuf Yusuf, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi da tsohon dan majalisa, Sanata Abdullahi Gumel ne ke tallata shi.

Yunkurin tsayar da shi wanda ya fara kafin sanatocin su tafi hutun sallah ya raba kan majalisar wacce ke da yan APC 71, PDP 37 da dan YPP daya.

A makon da ya gabata ne sanatoci suka tafi hutun sallah. Za su dawo a ranar Talata, 10 ga watan Mayu.

Jam’iyyar mai mulki ta tsayar da ranar 31 ga watan Mayu da 1 ga watan Yuni don yin zaben fidda gwaninta, inda a nan za a zabi wanda zai rike tutar jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Jonathan Zai Yi Takarar Shugaban Ƙasa a 2023, Ya Yi Rajista Da APC a Mazabansa, Majiya

Baraka a tsakanin manyan yan APC

An tattaro cewa yunkurin tsayar da Lawan ya haifar da baraka a tsakanin jiga-jigan APC a majalisar dattawan.

Daily Trust ta kuma rahoto cewa tuni yan majalisa da dama suka hade da wasu masu takarar kujerar shugaban kasar.

Misali Sanata Ali Ndume yana jagorantar yakin neman zaben Amaechi ne, Sanata Kashim Shettima yana jagorantar na Tinubu yayin da Sanata Kabiru Gaya ke tare da mataimakin Shugaban kasa Osinbajo.

Baya ga wadannan mutanen uku, akwai wasu yan majalisa da ke yiwa wasu yan takarar kamfen, don haka yunkurin gabatar da Lawan a matsayin dan takarar yarjejeniya yake rawa.

A wata hira da Sanata Ali Ndume ta wayar tarho, ya ce wadanda ke tallata takarar Lawan basu tuntube shi ba, yana mai cewa:

“Ba su zo ba saboda sun san matsayina.
“Bani da wata manufa kan Ahmad Lawan; takwarana ne amma bana goyon bayan rashin adalci. Ba zan goyi bayan koda dan uwana na jini ba. Fitar da dan arewa rashin adalci ne kuma daidai yake da wa’adi na uku. Dattawan arewa da ke tallata shi suna aikata hakan ne don rashin adalci.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Hadimin Buhari, Bashir Ahmad ya yi murabus daga kujerarsa

“Zagayen kudu ne kuma ya zama dole mu mara masu baya don cimma hakan. Wadanda ke tallata hakan sun bani kunya. Tuni na dauki matsayina tunma kafin na jone da Amaechi.”

Yayin da yake watsi da ikirarin cewa ana matsawa Lawan don ya shiga tseren shugabancin kasar, wani dan majalisa ya ce duk shiri ne na Lawan da wasu makusantansa yan tsiraru.

“Ba gaskiya bane cewa dattawan arewa ne tura shi. Shi ke tura kansa; idan ba haka ba, Ku ce masa ya kira sunan dattawan arewan. Su wanene?
“Kudirinsa ne kawai babu wanda ke tura shi, maimakon haka shine yake tura mutane a harkar. Suna kokarin gabatar da shi a matsayin dan takarar yarjejeniya kuma Za mu turje.”

Amma wani dan majalisa a sansanin Lawan sun ce lallai dattawan arewa ne ke neman ya fito.

2023: Gwamna Fayemi zai ayyana aniyar tsayawa takarar shugaban kasa a APC

A wani labarin kuma, gwamnan jihar Ekiti kuma shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, Kayode Fayemi zai bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin kasar a ranar Laraba a Abuja, kamar yadda jaridar Punch ta samo.

Kara karanta wannan

2023: Jonathan Ya Sauya Ra'ayinsa Kan Tikitin APC, Ya Nuna Alamun Zai Amince Ya Yi Takarar

Babban sakataren yada labaransa, Yinka Oyebode ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Talata.

A cewarsa, ayyanawar ta ranar Laraba mai taken ‘Unveiling My Nigeria Agenda’, za ta haifar da hasashe kan ko zai tsaya takarar Shugaban kasa ko a’a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng