2023: Gwamna Fayemi zai ayyana aniyar tsayawa takarar shugaban kasa a APC
- Gwamnan jihar Ekiti ya bayyana aniyarsa ta shiga jerin 'yan takarar shugaban kasa a zaben 2023 mai zuwa
- Gwamnan, wanda mamba ne a jam'iyyar APC ya ce zai magantu kan yiwuwar tsayawarsa takara a ranar Laraba 4 ga watan Mayu
- Ana ci gaba da samun jiga-jigan jam'iyyar APC da sauran jam'iyyu da ke nuna sha'awarsu ga mulkar Najeriya a 2023
Gwamnan jihar Ekiti kuma shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, Kayode Fayemi zai bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin kasar a ranar Laraba a Abuja, kamar yadda jaridar Punch ta samo.
Babban sakataren yada labaransa, Yinka Oyebode ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a ranar Talata.
A cewarsa, ayyanawar ta ranar Laraba mai taken ‘Unveiling My Nigeria Agenda’, za ta haifar da hasashe kan ko zai tsaya takarar Shugaban kasa ko a’a.
Oyebode ya ce shugaban nasa ya tattauna shirinsa na tsayawa takara da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, da sarakunan gargajiya da shugabannin siyasa a fadin jihohin kasar nan.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Dr Fayemi ya fara tuntuba da neman shawari ne a garin Owo, jihar Ondo, inda ya gana da Olowo na Owo, Mai Martaba Oba Ajibade Gbadegesin Ogunoye, kamar yadda TVC News ta ruwaito.
Bayan haka, Dr Fayemi ya gana da shugaban kungiyar Afenifere, Cif Reuben Fasoranti da sauran shugabannin kungiyar siyasa da zamantakewar kabilar Yarabawa, da suka hada da Cif Olu Falae da Cif Cornelius Adebayo a Akure, babban birnin jihar Ondo.
Zaben 2023: Jigon APC ya shiga jerin 'yan takarar shugaban kasa, zai sayi fom
A wani labarin, wani dan jam’iyyar APC mai mulki, Mista Gbenga Olawepo-Hashim ya bayyana aniyarsa ta neman ya gaji kujerar shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2023.
Olawepo-Hashim wanda ke da sha'awar daga tutar jam'iyyarsa a zaben shugaban kasa na shekara mai zuwa na shirin sayen fom din tsayawa takara a ranar Alhamis 5 ga watan Mayu a sakatariyar jam'iyyar da ke Abuja.
Ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai wacce Legit.ng ta samo.
Ya dage cewa duk da cewa kasar a halin yanzu Najeriya na durkushe cikin tsananin rashin isassun kayayyakin aiki saboda wasu dalilai, ya ce yayi imanin cewa zai kawo sauyi a kasar.
Asali: Legit.ng