2023: Gwamnan PDP ya ziyarci Obasanjo, ya ce ya gama shiri tsaf don ceto Najeriya
- Gwamna Emmanuel Udom na jahar Akwa Ibom ya kai ziyarar ban girma ga tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo
- Udom ya ziyarci babban jigon kasar ne domin sanar da shi kudirinsa na son gaje kujerar shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2023
- Ya kuma sha alwashin magance manyan kalubalen da kasar ke fuskanta idan har aka bashi damar yin haka
Ogun - Gwamnan jihar Akwa Ibom, Emmanuel Udom, ya ziyarci tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a ranar Talata, 3 ga watan Mayu, a gidansa da ke Abeokuta.
Udom ya ziyarci babban jigon kasar ne domin sanar da shi kudirinsa na son yin takarar shugaban kasa a babban zaben 2023 mai zuwa, jaridar The Cable ta rahoto.
Gwamnan ya sanar da Obasanjo cewa a shirye yake ya ceto kasar tare da daidaita abubuwa kasancewar yana da tarin gogewa a bangaren gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu.
Dan takarar ya ce za a iya magance manyan matsalolin da suka addabi Najeriya ta hanyar shugabanci mai cike da hankali, gaskiya da kuma kwarewa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya fadawa Obasanjo cewa idan aka ba shi dama, zai dauki matakai masu amfani don bunkasa tattalin arziki da kuma mayar da Najeriya yadda take a baya.
Dan siyasar na daya daga cikin yan takarar da ke neman daga tutar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zabe mai zuwa.
Zai yi fafutukar neman tikitin jam’iyyar tare da sauran yan takara kamar su Atiku Abubakar, Bukola Saraki, Nyesom Wike, Aminu Tambuwal, Bala Mohammed da sauransu.
Da yake martani, Obasanjo ya nuna godiya ga dan takarar shugaban kasar kan girmama shi da ya yi ta hanyar zuwa ya sanar da shi kudirinsa na yin takara, rahoton Vanguard.
Rashin gaskiya: Matsala ta da Saraki, Tambuwal da 'yan takaran Arewa - Gwamna Wike
A wani labarin, gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, a ranar Litinin, ya bayyana matsalarsa da tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki da gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal kan batun mika shugabancin kasar zuwa yankin kudu gabannin zaben 2023.
Wike ya ce ya sha goyon bayan yan takarar shugaban kasa daga arewa, inda yake mamakin dalilin da yasa wadanda ya marawa baya a zaben 2019 suke kara neman takarar shugaban kasa a 2023.
Ya bayyana hakan ne yayin da ya fito a sharin Politics Today na gidan talbijin din Channels.
Asali: Legit.ng