Shugaban kasa: Lissafi na iya canzawa a mintin karshe, watakila APC ta tsaida ‘Dan Arewa

Shugaban kasa: Lissafi na iya canzawa a mintin karshe, watakila APC ta tsaida ‘Dan Arewa

  • Ba abin mamaki ba ne a ga APC ta fasa tsaida ‘Dan kudu a matsayin ‘dan takarar shugaban kasa
  • Ganin yadda abubuwa su ke ta tafiya a jam’iyyar PDP, lissafin APC mai mulki na neman canzawa
  • Jam’iyyar APC za ta nemi duk yadda za ta doke PDP a zaben 2023, ta cigaba da mulkin Najeriya

Akwai alamun da ke nuna jam’iyyar APC ta na iya tsaida mutumin Arewa a matsayin wanda zai yi mata takarar shugaban kasa da PDP a zabe mai zuwa.

Punch ta fitar da rahoto a ranar Litinin da ya nuna cewa wasu kusoshin APC sun fara laluben ‘dan siyasa daga yankin Arewa mai karfi da za a iya ba takara.

Hakan na zuwa ne bayan la’akari da cewa hankalin PDP ya karkata wajen ganin daga Arewa su ka tsaida ‘dan takarar shugaban kasa domin su doke APC.

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: Wani Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a APC Ya Sake Janye Takararsa

Har zuwa yanzu, tunanin da ake yi shi ne daga bangaren kudu za a samu wanda zai nemi takara a APC, ganin Muhammadu Buhari daga shiyyar Arewa ya fito.

A wata hira da aka yi da shugaban APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya nuna cewa jam’iyya ba ta tsaida magana a game da yankin da za a kai takara ba.

Jaridar ta nemi jin ta bakin sakataren yada labarai na APC, Felix Morka, amma bai dauki waya ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban kasa Buhari
Buhari, Osinbajo da Lawan Hoto: www.thisdaylive.com
Asali: UGC

Akwai wannan maganar

Amma da aka zanta da shugaban VON wanda yana cikin wadanda aka kafa APC da su, Osita Okechukwu ya tabbatar da gaskiyar wannan rade-radin.

Osita Okechukwu ya ce akwai yiwuwar a hana ‘yan kudu takarar shugaban kasa a zaben fitar da gwani da jam’iyyar APC za ta gudanar a karshen Mayu.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Goodluck Jonathan ba zai yi takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC ba

The Cable ta rahoto Okechukwu ya na cewa dole APC ta iya wanke allonta domin zuwa yanzu ta rasa matsaya saboda tunanin yadda za ta doke PDP a 203.

Wani daga cikin sababbin shugabannin jam’iyyar APC na kasa, ya shaidawa 'yan jarida cewa ‘dan takara zai iya fitowa daga ko ina, muddin za a lashe zabe.

Masu neman takara a APC

Kawo yanzu manyan masu neman tikitin APC su ne; Asiwaju Bola Tinubu, Farfes Yemi Osinbajo, Rotimi Amaechi, Dr. Chris Ngige, da Gwamna Dave Umahi.

Sai kuma tsofaffin gwamnonin jihohi irinsu Sanata da Rochas Okorocha da Sanata Orji Uzor Kalu.

An fara maganar Ahmad Lawan

Kun samu labari cewa akwai yiwuwar a makon nan a ji cewa Dr. Ahmad Ibrahim Lawan zai tsaya neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC mai mulki.

Kafin a fara jita-jitar takarar Sanata Ahmad Lawan, Zuwa yanzu Gwamna Yahaya Bello ne kadai wanda ya fito daga bangaren Arewa da ke neman tikiti a APC.

Kara karanta wannan

Jonathan ya amsa kiran masoyansa, yau za a gabatar da fam din shiga takararsa a APC

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng