Ma'auni 6 da PDP ta yi amfani da su wajen soke takarar 2 daga cikin masu neman kujerar Buhari

Ma'auni 6 da PDP ta yi amfani da su wajen soke takarar 2 daga cikin masu neman kujerar Buhari

Batun soke takarar biyu daga cikin masu neman kujerar shugabancin kasar na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya zo ma wasu mambobin jam’iyyar dama yan Najeriya a bazata a ranar Juma’a, 29 ga watan Afrilu.

Tun bayan da tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark, wanda shine shugaban kwamitin tantance yan takarar ya bayar da sanarwar, yan Najeriya na ta so su san dalilin da yasa aka soke takarar mutanen.

Ma'auni 6 da PDP ta yi amfani da su wajen soke takarar 2 daga cikin masu neman kujerar Buhari
Ma'auni 6 da PDP ta yi amfani da su wajen soke takarar 2 daga cikin masu neman kujerar Buhari Hoto: @atiku
Asali: Twitter

Binciken da Legit.ng ta yi ya bayyana dalilin da yasa PDP ta datse mafarkin yan takarar shugaban kasar biyu.

Koda dai kwamitin tantance yan takarar bai bayyana sunayen yan takarar da aka sallama ba a yayin zantawa da manema labarai bayan shirin a ranar Juma’a, ya bayyana cewa an fitar da yan takarar ne saboda basu cike abubuwan da ake bukata domin hawa kujerar ba.

Kara karanta wannan

Wani dan takarar shugaban kasa ya karaya ya kai karar PDP kan kudin fom N40m

Ga ka’idojin da aka yi amfani da su a yayin tantance yan takarar:

1. Sahihancin rijistar zama dan jam'iyya na kowane dan takara

2. Nauyin aljihun yan takara

3. Matsayin karatun masu neman takara

4. Takardar haraji

5. Katin zabe

6. Tabbacin da ke nuna mutum dan kasa ne

PDP ta soke biyu daga cikin 'yan takararta na shugaban kasa

A baya mun kawo cewa jam’iyyar PDP ta soke biyu daga cikin masu neman tsayawa takarar shugaban kasa 17 da ke neman tikitin takara a zaben 2023, The Nation ta ruwaito.

‘Yan takarar biyu da aka soke za su yi asarar Naira miliyan 40 da kowannen su ya biya na fom din tsayawa takara.

Shugaban kwamitin tantance 'yan takarar shugaban kasa na PDP, Sanata David Mark NE ya sanar da dakatar da ‘yan takarar biyu a yammacin ranar Juma’a.

Kara karanta wannan

2023: 'Yan takarar gwamnan APC a Filato sun yi baranzanar sauya sheka saboda dalilai

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng