Labari mai zafi: PDP ta soke biyu daga cikin 'yan takararta na shugaban kasa
- Jam'iyyar PDP ta yi shara, ta soke 'yan takara biyu daga cikin masu neman tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023
- Jam'iyyar bata bayyana sunayen wadanda lamarin ya shafa ba, amma dai ta ce basu cancanta ba sam
- Hakan na nufin sun yi asarar kudin fom din takara akalla Naira miliyan 40 kowannensu, kamar yadda ya tabbata
Abuja - Jam’iyyar PDP ta soke biyu daga cikin masu neman tsayawa takarar shugaban kasa 17 da ke neman tikitin takara a zaben 2023, The Nation ta ruwaito.
‘Yan takarar biyu da aka soke za su yi asarar Naira miliyan 40 da kowannen su ya biya na fom din tsayawa takara.
Shugaban kwamitin tantance 'yan takarar shugaban kasa na PDP, Sanata David Mark NE ya sanar da dakatar da ‘yan takarar biyu a yammacin ranar Juma’a.
Sai dai Mark ya ki amincewa da bukatar ‘yan jarida na bayyana sunayen wadanda abin ya shafa da kuma dalilin rashin cancantarsu.
Da aka tambaye shi ko kwamitin tantancewar ya ba da wata shawara ga jam’iyyar ta maido da kudaden fom din Naira miliyan 80 da ‘yan takarar suka biya, Mark ya ce:
“Me ya sa jam’iyyar za ta mayar da kudaden?”
Karin bayani na nan tafe...
Asali: Legit.ng