2023: PDP ce dai kadai za ta kai 'yan Najeriya ga tudun mun tsira, inji Saraki

2023: PDP ce dai kadai za ta kai 'yan Najeriya ga tudun mun tsira, inji Saraki

  • Yayin da ake ci gaba da sa ran ganin 'yan takara daga jam'iyyun siyasar kasar nan, Bukola Saraki ya yi karin haske
  • Ya bayyana cewa, mafita ga 'yan Najeriya a yanzu dai itace ba PDP dama a zaben 2023 mai zuwa nan kusa
  • Ya bayyana dalilansa, tare da fadin irin romon dimokradiyya da PDP ta girkawa 'yan Najeriya a zaben na 2023

Gabanin zabukan 2023 a kasar nan, dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Dakta Bukola Saraki, a ranar Laraba, ya ce PDP ce kadai sahihiyar jam’iyyar siyasa da za ta ceto Najeriya da gaske daga tarin kalubalen da ke hana ruwa gudu da kawo ci gabanta mai dorewa.

Saraki ya bayyana hakan ne a wata hira da yayi da manema labarai na gidan gwamnati jim kadan bayan wata ziyarar sirri da ya kai wa Gwamna Ifeanyi Okowa a gidan gwamnatin Asaba, inji TheNation.

Kara karanta wannan

Kuri'u miliyan 11 ke jirana: Atiku ya bayyana yadda 'yan Najeriya ke kaunarsa

Bukola Saraki kan batun siyasar Najeriya da PDP
2023: PDP ce dai kadai za ta kai 'yan Najeriya ga tudun mun tsira, inji Saraki | Hoto: dailytrust.com
Asali: Depositphotos

A cewarsa, jam’iyyar PDP ta samar da sahihiyar hanya daya tilo da za ta ciyar da Najeriya gaba, ya kara da cewa gwamnatin PDP za ta tabbatar da turbar kasar inda za a samar da ayyuka masu ma’ana ga matasa.

Ya kara da cewa kasar na tafiya ba daidai ba bisa la’akari da kididdigar da ke fitowa a kowace rana, yana mai nuni da cewa matsalar tsaro a kasar ba ta samun sauki ba, ga kuma tabbacin cewa a kullum tsadar rayuwa na kara ta'azzara.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A kamalansa:

“Kamar yadda kuke gani, kasar na tafiya ba daidai ba bisa ga kididdigar da ke fitowa a kowace rana. Batun tsaro ba a magana a kasar ga kuma tsadar rayuwa na kara ta'azzara a kullum."

Daily Sun ta kara da cewa, da yake magana game da tsarin raba tikiri ga shiyya-shiyya a PDP, tsohon shugaban majalisar dattawan ya ce:

Kara karanta wannan

Kowa tashi ta fishe shi: Shugaban PDP ya nunawa Atiku ba sani ba sabo

"Kamar yadda kuka sani, hakan ya je ga kwamitin shiyya kuma sun yi rahotonsu sun mika shi ga kwamitin zartarwa na jam’iyyar (NEC) na kasa.
“Don haka, NEC ita ce babbar hukumar jam’iyyarmu kuma ba zan iya yin magana a kan hakan ba har sai mun san abin da hukumar za ta yanke.”

Kuri'u miliyan 11 ke jirana: Atiku ya bayyana yadda 'yan Najeriya ke kaunarsa

A wni labarin, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya bukaci jam’iyyar PDP da ta bashi dama a zaben fidda dan takararta na shugaban kasa saboda shine dan takara mafi cancanta da zai kawo mata kujerar.

Da yake jawabi ga mambobin kwamitin NWC na jam’iyyar a ranar Alhamis, 28 ga watan Afrilu, Atiku ya ce ya kamata a yi la'akari da shi saboda tuni ya mallaki kuri’u miliyan 11 da ke jiransa, Daily Trust ta rahoto.

Atiku ya ce: “Ni ne dan takara mafi cancanta. A tashin farko Mista Ciyaman, wannan mutum ne wanda kuri’u miliyan 11 ke jiransa. Kuma ina ganin, a matsayin jam’iyya, ya kamata ku bani dama a tashin farko amma muna a tsari ne na damokradiyya.

Kara karanta wannan

An sake samun wani babban Gwamna a APC da yake tunanin fitowa Shugaban kasa

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.