2023: Jam’iyyar PDP ta na hannun Shugaban Jam’iyyar da Kwankwaso ya bari inji Kotu
- Babbar kotun tarayya ta yi zama a kan shari’ar Shehu Wada Sagagi da uwar jam’iyyar PDP a Abuja
- Alkali ya kara tabbatar da cewa har yanzu Sagagi ne ingantaccen shugaban PDP na reshen Kano
- Mai shari’a ya bukaci shugabannin PDP su rusa duk wani kwamitin rikon kwarya da suka kafa
Abuja - Babbar kotun tarayya da ke zama a garin Abuja ta tabbatar da Alhaji Shehu Wada Sagagi a matsayin shugaban jam’iyyar PDP na reshen Kano.
Jaridar Daily Nigerian ta ce kotu ta maida ‘yan majalisar Shehu Wada Sagagi a kan kujerunsu, har zuwa lokacin da za a karkare sauraron wannan karar.
Alkali mai shari’a Taiwo O. Taiwo ya karbi rokon da Shehu Wada Sagagi da ‘yan majalisarsa su ka gabatar na cewa ka da a sauke su daga mukamansu.
Kamar yadda wata sanarwa a Facebook ta nuna, Mai ba shugaban PDP na Kano shawara a kan harkar shari’a, Isah Wangida ya yi karin haske kan zaman.
Mun samu nasara - Barista Isah Wangida
Barista Isah Wangida ya ce a ranar Talata wani lauya ya tabbatarwa Alkali cewa uwar jam’iyya ba ta canza ‘yan majalisar da ke gudanar da aikin PDP ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewar Wangida, kotu ta saurari duka bangarorin a zaman da aka yi na ranar Alhamis bayan lauyoyin PDP sun canza magana ta bakin wani lauyan.
Adedamola Fanokun ne ya fara cewa ba a canza shugabanni ba, a yau kuma sai aka ji A.O. Dada yana cewa an yi hakan, kuma ya roki a tabbatar da tsige su.
Amma mai shari’a Taiwo ya zartar da cewa idan har an nada wasu shugabannin dabam, daga yau an sauke su domin har yanzu ba a san da zaman wasunsu ba.
Hadimin shugaban jam’iyyar hamayyar ya yi kira ga ‘ya ‘yan PDP da magoya baya da su kwantar da hankalinsu domin har gobe su Hon. Sagagi ne ke kan iko.
A cewar Lauyan, karya ta karewa masu ja da shugabannin jam’iyya domin a yau an tabbatar da ingancin majalisarsu, akasin matakin da NWC ta dauka a baya.
Tarihin shari’ar PDP v Sagagi
A baya babban kotun tarayyar ta gargadi shugabannin PDP na kasa a kan rantsar da shugabannin riko alhali wa’adinsu Shehu Sagagi a ofis bai kare ba.
Amma jam’iyyar hamayyar ba tayi wa Alkalin kotu biyayya ba, sai ta sauke duk shugabannin da ke rike da PDP a matakin jiha, kananan hukumomi da kuma mazabu.
Idan har za ku iya tunawa, hukumar INEC ta ki karbar wannan canjin shugabanci da ake neman yi, ta ce Shehu Sagagi kurum ta sani a matsayin shugaban jam'iyya.
Asali: Legit.ng