An jefa jam’iyyar PDP cikin ala-ka-kai a Kano, kotu tace a ruguza duka sababbin shugabanni

An jefa jam’iyyar PDP cikin ala-ka-kai a Kano, kotu tace a ruguza duka sababbin shugabanni

  • Shugabannin jam’iyyar PDP na kasa (NWC) sun ruguza majalisar Alhaji Shehu Wada Sagagi a Kano
  • Da aka je kotu sai aka ji lauyan jam’iyyar PDP, Adedamola Fanokun ya na karyata wannan zance
  • Alkali ya gargadi shugabannin PDP su guji canza shugabannin PDP na reshen jihar Kano a yanzu

Kano - Lauyan da yake kare jam’iyyar PDP a gaban kotu a shari’ar da ake yi a kotun tarayya na Abuja, ya musanya zargin sauya shugabannin PDP na Kano.

Jaridar Daily Nigerian ta rahoto Adedamola Fanokun ya fadawa Alkali cewa uwar jam’iyya ba ta cire su Shehu Sagagi, ta nada wasu sababbin shugabanni ba.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da majalisar NWC ta kasa ta ruguza daukacin shugabannin jam’iyyar PDP a mazabu, kananan hukumomi da jiha a Kano.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Kwankwaso ya koma NNPP, ta yiwu Tinubu kuma ya koma SDP, inji majiya

Daukar wannan mataki ke da wuya, sai hukumar INEC ta aiko takarda, ta na cewa ba ta san da zaman kwamitin rikon kwaryan da uwar jam’iyya ta nada ba.

Hukumar zabe ta bayyana wannan ne ganin cewa kotun tarayyar mai zama a Abuja ta bada umarnin dakatar da taba shugabannin sai an kammala shari’a.

Ba a nada wasu shugabanni ba - Adedamola Fanokun

Da aka dawo za a cigaba da shari’a a gaban Alkali Taiwo O. Taiwo, sai Adedamola Fanokun ya ce sam ba a rantsar da wasu shugabanni na dabam a Kano ba.

Shehu Wada Sagagi
Shugaban jam’iyyar PDP a Kano, Shehu Wada Sagagi Hoto: @FreedomRadioNigeria
Asali: Facebook

Taiwo Taiwo ya bukaci lauyan ya fadi gaskiya, amma ya hakikance a kan sam wanda yake karewa a kotu ba su sauke Sagagi, ko an nada kwamitin riko ba.

Kara karanta wannan

Neman kujerar Shugaban kasa ya barka Atiku, Saraki da ‘Yan takarar PDP, kai ya rabu 3

Bayan nan, Sahelian Times ta rahoto Taiwo ya ja kunnen lauyan cewa su (PDP) su guji saba masa, tare da kira ga wanda ake karewa, ya janye matakin da ya dauka.

“Ni Alkali ne mai bin doka, wanda ya yarda da doka. Ka fadawa wadanda ka ke karewa, idan har sun saba mani bayan umarnin kotu, su janye matakin da suka dauka.”

- Taiwo O. Taiwo.

A karshe Alkalin ya daga wannan shari’a zuwa ranar 28 ga watan nan na Afrilu. Ana sa ran nan da kusan makonni uku za a sake yin wani zama a kotun da ke Abuja.

Sababbin shugabannin PDP

Rahoton ya ce sababbin shugabannin riko da PDP NWC ta nada a Kano su ne; Alhaji Ibrahim Aminu Daniya, Hajiya Ladidi Dangalan; da Hon. Aminu Abdullahi Jungau.

Ragowar sun hada da Mukhtar Mustapha Balarabe, Abdullahi Isa Sulaiman da Baba Lawal Aliyu. Legit.ng Hausa ta ga hotunan bikin rantsarwar da aka yi a garin Abuja.

Kara karanta wannan

Rigingimu na neman ratsa PDP, ‘Ya ‘yan Jam’iyya su na zargin shugabanninsu da zagon-kasa

Asali: Legit.ng

Online view pixel