Ku shigo NNPP: Kwankwaso ya yi kira ga matasa su shigo NNPP domin ceto Najeriya

Ku shigo NNPP: Kwankwaso ya yi kira ga matasa su shigo NNPP domin ceto Najeriya

  • Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su shigo jam’iyyar da shiga kwanan nan; NNPP
  • Tsohon jigon na PDP ya bayyana cewa sabuwar jam’iyyar za ta biya bukatun ‘yan Najeriya da fiye da sauran jam'iyyu
  • Kwankwaso a yayin da yake zayyana neman kuri’u a zabe mai zuwa, ya bukaci matasa da su je karbar katin zabe su yi zabe kamar yadda yake 'yancinsu ne

Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi'u Kwankwaso, ya bukaci 'yan Najeriya musamman matasa da su shiga jam'iyyar NNPP don dawo da Najeriya da samar da rauwa mai kyau da 'yan kasa ke so.

Kwankwaso wanda ya yi wannan kiran yayin babban taron jam’iyyar na kasa da aka gudanar a Abuja, ya bayyana cewa jam’iyyar NNPP ta yi fice wajen ceto al’ummar kasar, inji rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Yanzu nan: Sanata Kwankwaso ya aikawa Jam’iyya takardar barin PDP, ya bayyana dalilansa

Tsohon gwamnan Kano ya yi kira a shigo NNPP
Ku shigo NNPP: Kwankwaso ya yi kira ga matasa su shigo NNPP domin ceto Najeriya | Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

A cewar tsohon gwamnan, sabuwar jam’iyyar za ta tabbatar da ayyukan yi, da ingantaccen ilimi ba tare da yajin aikin ba, da dai sauransu ga matasan kasar nan.

Kiran Kwankwaso ga matasa

Ya kuma bukaci matasa da su yi rajista da jam’iyyar da kuma hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) domin su karbi katin zabe su zabi jam’iyyar a 2023.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yace:

"Wannan NNPP din iska mai kyau ce ga 'yan Najeriya saboda 'yan kasar suna neman sabuwar Najeriya ne kuma mafi inganci tun da sun gaji da halin da ake ciki."

Kwankwaso ya ce idan har aka yi haka, duk kalubalen da ake fuskanta a yanzu za a manta da shi idan NNPP ta samu mulki.

Ya kara da cewa:

"Wannan jam'iyyar ta dukufa wajen gyara kurakuran da aka yi a baya kuma da goyon bayanku za mu samu ingantacciyar Najeriya."

Kara karanta wannan

Duk da ‘Dan takararsa bai yi nasara ba, Tinubu ya taya Adamu murnar zama Shugaban APC

Daga Komarwarsa NNPP, Kwankwaso ya samu muhimmim muKami

A jiya, an naɗa tsohon gwamnan Jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a matsayin jagoran jam'iyyar New Nigeria People's Party (NNPP), The Nation ta ruwaito.

The Punch ta ruwaito cewa an amince da nadin Kwankwaso ne a wurin taron jam'iyyar a Abuja, kwana ɗaya bayan ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar PDP a Abuja.

Mabiya tsohon gwamnan na Kano suma sun samu mukamai a kwamitin jam'iyyar na NEC mai mutane 39 da za su jagoranci harkokin jam'iyyar.

Farfesa Rufai Alkali, masanin kimiyyar siyasa kuma tsohon sakataren watsa labarai na PDP ne ya zama shugaban NNPP na ƙasa.

Yan takarar shugaban kasa uku na PDP sun gana da IBB kan batun wanda zai gaji Buhari a 2023

A wani labarin, 'yan takarar kujerar shugaban ƙasa ƙarƙashin inuwar PDP guda uku sun gana da tsohon shugaban ƙasa a mulkin Soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida mai ritaya.

Kara karanta wannan

Jerin shugabannin da suka yi nasara, da wadanda suka sha kasa a zaben jam’iyyar APC

Daily Trust ta rahoto cewa yan takarar, gwamna Aminu Tambuwal na Sokoto, gwamna Bala Muhammed na Bauchi da tsohon gwamnan Kwara, Bukola Saraki, sun tattauna da IBB ne kan yuwuwar yin sulhu.

Da yake jawabi a madadin sauran yan tawagar, Saraki ya ce sun ziyarci IBB ne domin neman shawarinsa da kuma sa su a hanyar fitar da ɗan takara ɗaya da kowa zai amince.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.