Karin bayani: Sanatan APC ya tura wa majalisa wasika, yana son gaje Buhari a zaben 2023

Karin bayani: Sanatan APC ya tura wa majalisa wasika, yana son gaje Buhari a zaben 2023

  • Sanata mai wakiltar Ogun ta tsakiya ya bayyana aniyarsa ta son gaje kujerar Buhari a zaben 2023 mai zuwa
  • Ya bayyana hakan ne a cikin wata wasikar da shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan ya karanta a zauren majalisar
  • Ya zuwa yanzu dai akwai sama da 'yan siyasar APC 15 da suka bayyana aniyarsu ta gaje kujerar Buhari a 2023

FCT, Abuja - Majalisar dattawa ta karbi wasikar nuna sha'awar tsayawa takarar shugaban kasa daga jigon APC, kuma sanata mai wakiltar Ogun ta tsakiya Ibikunle Amosun.

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ne ya karanta wasikar yayin zaman majalisa na yau Laraba 27 ga watan Afrilun 2022.

Sanatan APC ya tsaya takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC
Da duminsa: Sanatan APC ya tura wa majalisa wasika, yana son gaje Buhari a zaben 2023 | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Sanarwar da Legit.ng Hausa ta samo daga majalisar ta bayyana cewa:

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Karamin Ministan Ilmi, Emeka Nwajiuba, ya saya Fom din takara shugaban kasa N100m

"Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan ya karanta wasikar sanarwa daga Sanata mai wakiltar Ogun ta tsakiya, Ibikunle Amosun, inda ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar Shugabancin Tarayyar Najeriya a karkashin jam’iyyar APC."

Jam'iyyar APC dai na kara samun karin 'yan takarar da ke da burin gaje kujerar Buhari a zaben 2023 mai zuwa idan Allah ya kaimu.

Hanzari ba gudu ba: NDLEA ta nemi a fara yiwa 'yan siyasan APC gwajin shan kwayoyi

A wani labarin, shugaban hukumar NDLEA Birgediya Janar Buba Marwa (rtd) ya rubuta wasika ga shugaban jam’iyyar APC Abdullahi Adamu, inda ya bukaci a baiwa jami’an NDLEA damar gudanar da gwajin tabbacin kubuta daga shan kwaya ga 'yan siyasa da ke neman takara.

Marwa ya ce a lokacin da PDP da sauran jam’iyyu za su gudanar da zabukan fidda gwani, zai kuma rubuta musu wannan bukata ta gwajin.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Jigo a majalisa, sanatan PDP daga Sokoto ya sauya sheka zuwa APC

Shugaban na NDLEA wanda ya ke jawabi a wajen bikin karramawar kwata-kwata na farko a 2022 na hukumar a Abuja ya bayyana cewa gwajin shan kwaya ya zama dole don tabbatarwa da samar da ‘yan siyasa masu muhimmanci ofisoshin gwamnatin kasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.