Jerin Sunaye Jiga-Jigan PDP da zasu tantance yan takarar shugaban ƙasa a 2023
- Tsohon shugaban majalisar Dattawa, David Mark, shi zai jagoranci kwamitin mutum 9 da zai tantance yan takarar shugaban ƙasa a PDP
- Sakataren tsare-tsare na PDP ta ƙasa, Umar Bature, ya fitar da sunayen sauran mambobin kwamitin da ranar aikin su
- Sanarwan ta kuma bayyana kafa kwamitoci Shida da zasu tantance yan takarar gwamna a dukkan sassan ƙasar nan
Abuja - An bayyan sunan tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata David Mark, a matsayin shugaban kwamitin tantance yan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP.
Sakataren tsare-tsare na PDP ta ƙasa, Umar Bature, shi ya bayyana kwamitin mai ƙunshe da mambobin mutum 9 a wata sanarwa da ya sa wa hannu, kamar yadda Premium Times ta rahoto.
Kwamitin sun haɗa da tsohon gwamnan Ribas, Celestine Omehia; babban Lauya, Mike Ahamba; tsohon gwamnan Ondo, Olusegun Mimiko, masanin doka, Edward Ashiekaa da kuma wata yar fafatukar kare haƙƙin mata, Hilda Makonto.
Tikitin shugaban kasa: PDP za ta tantance Atiku, Saraki, Tambuwal da wasu yan takara 14 a ranar Juma’a
Sauran sune tsohon hadimin shugaban ƙasa, Akilu Indabawa, Esther Uduehi da kuma Hassana Dikko
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sanarwan na zuwa ne kwanaki uku bayan jam'iyyar PDP ta kawo ƙarshen sayar da Fom ɗin nuna sha'awar takara a zaɓen dake tafe.
Kwamitin tantancewan zai gudanar da aikinsa ne a Legacy House dake Maitama, birnin tarayya Abuja ranar 29 ga watan Afrilu, 2022.
Ƙarƙashin jagorancin David Mark, ana tsammanin kwamitin zai tantance yan takara 17, waɗan da suka sayi fom ɗin takara kuma suka maida shi kafin cikar wa'adi.
Haka nan kuma jam'iyyar PDP ta kafa kwamitin ɗaukaka ƙara kan tantancewa, wanda ke karkashin jagorancin shugaban jam'iyya na ƙasa, Dakta Iyorcha Ayu.
Sauran kwamitocin da PDP ta kafa
PDP ta kuma kafa kwamitoci Shida da zasu jagoranci tantace yan takarar kujerar gwamna a shiyyoyin Najeriya shida, kowane kwamiti na da mambobi 7.
Tsohon gwamnan Kaduna, Ahmed Makarfi, shi zai shugabanci kwamitin tantance yan takarar gwamna a yankin kudu maso yamma, yayin da gwamnan Bayelsa, Diri Douye, zai shugabanci kwamitin kudu maso kusu.
Tsohon mataimakin gwamnan Abiya, Acho Nwakanma, shi aka naɗa ya jagoranci kwamitin yankin kudu maso gabas, tsohon mataimakin gwamnan Ondo, Oluwateru Omolade, zai shugabanci kwamitin arewa maso yamma.
Tsohon minista Abdu Bulama kwamitin arewa maso gabas, sai kuma Tim Eneje wanda zaia shugabanci kwamitin arewa ta tsakiya, kamar yadda The Cable ta rahoto.
Bayan haka, PDP ta sanar da kwamitocin da zasu tantance yan takarar kujerun yan majalisun tarayya da na jihohi 36 dake faɗin Najeriya.
Yaushe kwamitocin zasu yi aikin su?
Sakataren Tsare-tsare ya ce za'a gudanar da aikin tantance yan takarar majalisun tarayya da na jihohi a dukkan manyan biranen jihohin ƙasar nan a ranar 27 ga watan Afrilu, ban da jahar Anambra.
Na gwamnoni kuma zai gudana a Sakatariyar PDP ta kowace shiyya in ban da shiyyar Arewa maso yamma, wanda zai gudana a Sakatariyar kasa duk a ranar 28 ga watan Afrilu.
A wani labarin kuma Masu cin gajiyar N-Power sun yi karo-karo, sun tara Miliyoyin Naira domin taimaka wa ɗan takara gwamnan Kano
Ma'aikatan tsarin N-Power a jihar Kano sun taimaka wa Sha'aban Sharaɗa da kuɗi miliyan N10m don cimma burinsa a 2023.
Sharaɗa, ɗan majalisa mai wakilatar mazaɓar Kano Municipal, ya na daga cikin yan takarar gwamnan Kano karkashin APC.
Asali: Legit.ng