Masu cin gajiyar N-Power sun yi karo-karo, sun tara Miliyoyin Naira zasu siya wa ɗan takara Fom a Kano

Masu cin gajiyar N-Power sun yi karo-karo, sun tara Miliyoyin Naira zasu siya wa ɗan takara Fom a Kano

  • Ma'aikatan tsarin N-Power a jihar Kano sun taimaka wa Sha'aban Sharaɗa da kuɗi miliyan N10m don cimma burinsa a 2023
  • Sharaɗa, ɗan majalisa mai wakilatar mazaɓar Kano Municipal, ya na daga cikin yan takarar gwamnan Kano karkashin APC
  • Wata ƙungiya FJK ta bi sahun masu cin gajiyar shirin, ta tara wa ɗan majalisar wasu miliyan N10m na daban

Kano - Aƙalla yan Najeriya 2,700 dake cin gajiyar tsarin N-Power a jihar Ƙano ne suka yi karo-karon tara kudi miliyan N10m domin goyon bayan takarar gwamnan Sha'aban Sharaɗa, mamba a majalisar wakilan tarayya.

Wannan na zuwa ne bayan wata ƙungiyar ma'aikata duk a jihar Kano wacce ake wa laƙabi da Fitilar Jama’ar Kano (FJK) ta tattara Miliyan N10m domin taimaka wa cikar burinsa na zama gwamna.

Kara karanta wannan

APC ta samu babban cikas, dubbannin masoyan Buhari sun koma bayan takarar Kwankwaso a 2023

Shirin N-Power.
Masu cin gajiyar N-Power sun yi karo-karo, sun tara Miliyoyin Naira ga ɗan takarar gwamnan Kano Hoto: Dailytrust.com
Asali: UGC

Honorabul Sha'aban Sharada, a yanzu haka shi ne ɗan majalisa mai wakiltar Kano Municipal a majalisar wakilan tarayyan Najeriya, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Haka nan kuma Sharaɗa ya na daga yan takarar dake hangen kujerar gwamnan jihar Kano ƙarƙashin inuwar jam'iyyar APC a zaɓen 2023 dake tafe.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ta ya ma'aikata suka iya haɗa makudan kudi haka?

Da yake miƙa wa ɗan majalisan cakin kudin a madadin sauran ma'aikatan N-Power, shugaban su na jihar Kano, Abba Lawan, ya faɗi yadda suka yi namijin kokari suka haɗa kudin.

A jawabinsa ya ce:

"Kowane ma'aikaci ɗaya daga cikin mu ya ba da gudummuwar Naira Dubu N5,000 ta hanyar aje Dubu Ɗaya a kowane wata na tsawon watanni biyar."

A bangaren sa, yayin da yake karɓan gudummuwar a madadin ɗan majalisan, ɗaya daga cikin shugabannin FJK, Mansur Kurugu, ya ce kungiyarsu ba'a barta a baya ba, ta haɗa miliyan N10m don tallafawa ɗan majalisan.

Kara karanta wannan

Ana Shirin Sallah: Yan bindiga sun kashe Kwamandan jami'an tsaro, sun tarwatsa mutanen gari a Zamfara

A wani labarin kuma Fitattun Attajirai biyu sun lale miliyan N200m zasu siyawa mutum biyu Fom ɗin takarar shugaban ƙasa a APC

Wasu yan kasuwa guda biyu yan asalin jihar Abia sun shirya lale makudan kuɗi Miliyan N200m don siya wa mutum biyu Fom a APC.

A wata sanarwa da suka fitar a Abuja , fitattun Attajiran sun ce sun gano kwarewa da salon mulki a jikin Sanata Ahmad Lawan da Orji Kalu.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel