Tikitin shugaban kasa: PDP za ta tantance Atiku, Saraki, Tambuwal da wasu yan takara 14 a ranar Juma’a
- Yayin da guguwar babban zaben kasar na 2023 ke kara kadowa, jam'iyyar PDP za ta fara tantance yan takararta na shugaban kasa a ranar Juma'a mai zuwa
- Babbar jam'iyyar adawa ta kasar za ta tantance yan takara 17 wadanda za su fafata wajen mallakar tikitinta na zaben shugaban kasa
- Shirin tantancewar zai gudana ne a hedkwatar yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar da ke Legacy House, Abuja
A ranar Juma’a mai zuwa ne jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) za ta tantance yan takara 17 da ke fafutukar mallakar tikitin shugaban kasa na jam’iyyar gabannin zaben 2023.
Tsohon shugaban majalisar dattawa, Cif David Mark, shine shugaban kwamitin mutum tara da za su gabatar da shirin tantance yan takarar, jaridar The Nation ta rahoto.
Yan takarar da za a tantance sune:
1. Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
2. Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki
3. Tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi
4. Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal
5. Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Pius Anyim
6. Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed
7. Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike
8. Gwamnan jihar Akwa, Ibom Udom Emmanuel
9. Fitaccen masanin masana’antu, Mazi Sam Ohuabunwa
10. Tsohon shugaban banki a kasar, Mohammed Hayatu-Deen
11. Babban likita mazaunin turai, Nwachukwu Anakwenze
12. Mawallafin mujallar Ovation Magazine, Dele Momodu
13. Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose
14. Cosmos Ndukwe
15. Charles Ugwu
16. Chikwendu Kalu
17. Tariele Diana
Jadawalin ayyukan da sakataren jam’iyyar PDP na kasa, Umar Bature, ya fitar ya nuna cewa za a gudanar da taron tantancewar ne a Legacy House da ke Abuja, hedkwatar yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar.
Har ila yau, daga cikin wadanda za a tantance a Abuja harda dukkanin yan takarar gwamna, majalisun dokokin jiha da na tarayya a dukkanin jihohi bakwai da ke yankin arewa maso yamma.
Jihohin sun hada da Sokoto, Kano, Kaduna, Katsina, Jigawa, Kebbi da Zamfara. An shirya tantance su ne a ranar Laraba da Alhamis.
Za a aiwatar da shirin tantancewar na sauran jihohi a sakatariyar jam’iyyar na yanki a wannan rana.
Mambobin kwamiin sune Cif Celestine Omehia; Cif Mike Ahamba, SAN; Dr. Olusegun Mimiko; Edward Ashiekaa, SAN, da Misis Hilda Makonto.
Sauran mambobin sune Dr. Akiku Indabawa, Hajiya Hassana Dikko, Dr. Esther Uduehi yayinda Ms. Chinedu Nwachukwu za ta yi aiki a matsayin sakatariyar kwamitin.
Shugaban kasa a 2023: Ban yarda da tsarin karba-karba ba – Gwamna Bala Mohammed
A wani labari, gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya bayyana cewa bai yarda da tsarin karba-karba ba gabannin zaben shugaban kasa na 2023 amma maimakon haka ya ce abun da ya kamata a mayar da hankali a kai shine neman shugaba da zai iya jagorantar Najeriya.
Osinbajo, Tambuwal da sauran 'yan takarar shugaban kasa 10 da basu halarci taron Iftar din Aisha Buhari ba
Gwamna Bala ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talbijin na Channels a shirin ‘Sunday Politics’.
Hakan na zuwa ne yan kwanaki bayan kungiyar dattawan arewa ta zabe shi da tsohon shugaban majalisar dattawa a matsayin yan takarar yarjejeniya na jam’iyyar PDP.
Asali: Legit.ng