Shugaban kasa a 2023: Ban yarda da tsarin karba-karba ba – Gwamna Bala Mohammed

Shugaban kasa a 2023: Ban yarda da tsarin karba-karba ba – Gwamna Bala Mohammed

  • Gabbanin zaben shugaban kasa na 2023 gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya nuna rashin amincewarsa da tsarin karba-karba
  • Mohammed ya ce babban abun damuwa shine yadda za a samar da shugaba wanda zai iya jagorantar Najeriya yadda ya kamata
  • Gwamnan na Bauchi ya kuma ce zai yarda ya janyewa Bukola Saraki ne idan har ya tabbatar masa da cewar zai iya shugabantar Najeriya fiye da shi

Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya bayyana cewa bai yarda da tsarin karba-karba ba gabannin zaben shugaban kasa na 2023 amma maimakon haka ya ce abun da ya kamata a mayar da hankali a kai shine neman shugaba da zai iya jagorantar Najeriya.

Gwamna Bala ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talbijin na Channels a shirin ‘Sunday Politics’.

Kara karanta wannan

Jerin yan takarar shugaban kasa 5 da suka ce Ubangiji ne ya kira su domin yin takara

Hakan na zuwa ne yan kwanaki bayan kungiyar dattawan arewa ta zabe shi da tsohon shugaban majalisar dattawa a matsayin yan takarar yarjejeniya na jam’iyyar PDP.

Shugaban kasa a 2023: Ban yarda da tsarin karba-karba ba – Gwamna Bala Mohammed
Shugaban kasa a 2023: Ban yarda da tsarin karba-karba ba – Gwamna Bala Mohammed Hoto: Premium Times
Asali: UGC

A cewarsa, an bukaci shi da Saraki su yanke shawara kan wanda zai zama dan takara da zai wakilci yankin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yayin da yake bayyana cewa yana da tarin ilimi da kwarewa don jagorantar Najeriya, ya ce zai janyewa Saraki ne idan ya tabbatar masa da cewar zai iya yin aikin fiye da shi a 2023.

Da aka tambaye shi ko zai janyewa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, wanda ake ganin yana daya daga cikin manyan yan takarar da ke hararar kujerar, Bala ya ce:

“Me zai hana shi Atiku ya janye mani.”

Rahoton ya kara da cewa, Bala ya yi bayanin cewa mutum daya tilo da zai janyewa shine Goodluck Jonathan idan ya ayyana aniyarsa ta yin takarar shugaban kasa.

Kara karanta wannan

2023: Shehu Sani ya hango yadda APC da PDP za su zabi 'yan takarar shugaban kasa

Ya ce:

“Ina nan akan bakata ta kin yin takara da Jonathan.”

Aisha Buhari na so mata su zama abokan takarar masu neman kujerun shugabanci a 2023

A wani labari na daban, Uwargidar shugaban kasa, Aisha Buhari, ta bukaci jam’iyyun siyasa da su dunga duba yiwuwar tsayar da mata a matsayin abokan takarar masu neman kujerun shugabanci a zaben kasar.

Aisha ta bayyana hakan ne yayin da take jawabi a daren ranar Asabar, 23 ga watan Afrilu, lokacin da ta karbi bakuncin masu neman takarar shugaban kasa daga jam’iyyu daban-daban a wajen buda baki a fadar shugaban kasa, Abuja, jaridar The Guardian ta rahoto.

Uwargidar shugaban kasar ta shirya taron buda bakin ne domin ba masu neman takarar damar wanzar da soyayya da farin ciki a tsakaninsu a cikin wannan wata ta Ramada da kuma kokarin hada kan kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng