Jonathan na shirin komawa APC, sannan ya ayyana niyyar takara kujerar shugaban kasa

Jonathan na shirin komawa APC, sannan ya ayyana niyyar takara kujerar shugaban kasa

  • Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan na shirin komawa jam'iyyar All Progressives Congress (APC)
  • Goodluck Jonathan dai dan jam'iyyar PDP ne amma cikin yan shekarun baya ya daina halartan tarukan PDP
  • Jam'iyyar APC har yanzu tana sayar da Fam din takara a farashin naira milyan dari

Da alamun komai ya kankama na tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya ayyana niyyar takara kujeran shugaban kasa a 2023 karkashin jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa Jonathan ya amsa kiran wasu jiga-jigai a APC da wasu a fadar shugaban kasa na ya koma APC kuma ya shiga takara.

Rahoton ya ce majiyoyi na kusa da tsohon shugaban kasa da yammacin jiya sun bayyana cewa an shirya komai don komawar APC gabanin zaben fidda gwanin ranar 30 da 31 ga Mayu, 2022.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Amaechi ya bayyana abun da zai yi ga duk wanda Buhari ya zaba

Tabbatar da hakan, daya daga cikin majiyoyin wanda ya bukaci a sakaye sunansa yace:

"Ba wai tsohon Shugaban Jonathan ke so ba, wasu jiga-jigai a APC ke kiransa ya fito takara. Ina ga jira kawai yake a kammala shirye-shiryen kafin ya ayyana niyyar takara."
"Kowa ya san tsohon shugaban kasan ba zai yanke shawara irin wannan a kurarren lokaci kamar haka ba idan bai da tabbaci."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jonathan
Jonathan na shirin komawa APC, sannan ya ayyana niyyar takara kujerar shugaban kasa
Asali: Twitter

Hakazalika an tattaro cewa APC na shirin basa dama shiga duk da dokar jam'iyyar ta ce sai mutum ya yi shekara biyu a jam'iyya zai iya takara.

Amma dokar ta baiwa shugabannin daman yafewa kowani mutum bukatar kasancewa cikin jam'iyyar tsawon shekaru biyu.

Dole ka tsaya takara: Masoya Jonathan sun mamaye ofishinsa, suna neman gafara

Yayin da Najeriya ke kara kusanto da babban zaben 2023, a ranar Juma'a masu zanga-zangar sun mamaye ofishin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a Abuja, suna kira gare shi da ya ayyana tsayawa takarar shugaban kasa a 2023.

Jama'ar sun kunshi maza da mata da matasa, inda suka mamaye ofishin dauke da alluna da takardu na neman tsohon shugaban kasar ya shiga takarar shugaban kasa

Asali: Legit.ng

Online view pixel