Wata Sabuwa: Ta sake kacamewa a APC, Sanata Adamu ya dakatar da dukkanin daraktocin jam'iyya

Wata Sabuwa: Ta sake kacamewa a APC, Sanata Adamu ya dakatar da dukkanin daraktocin jam'iyya

  • Sabon shugaban jam'iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu ya dakatar da dukkannin daraktocin sakateriyar jam'iyyar
  • Tun ranar da ya karba ragamar mulki, ya sanar da cewa ba zai yi amfani da tsoffin tsarika ba kuma ba zai lamunci gazawar aiki ba
  • Daga cikin daraktocin da aka dakatar, akwai daraktocin gudanarwa, tsari, jindadi da walwala, shari'a da yada labarai

FCT, Abuja - Wata sabuwa ta sake kacamewa a gidan Buhari inda hankula suka tashi a sakateriyar jam'iyyar APC ta kasa a ranar Juma'a sakamakon hukuncin shugaban jam'iyyar na kasa, Sanata Abdullahi Adamu inda ya bukaci dukkan daraktocin jam'iyyar da su dakata da aiki har sai baba ta gani.

Bayan Adamu ya hau karagar shugabancin jam'iyyar a ranar 1 ga watan fairilu, ya bayyana cewa akwai yuwuwar ya sake gyara tsarin ssakateriyar jam'iyyar ta kasa.

Kara karanta wannan

2023: Mataimakin gwamnan Katsina ya yi murabus daga mukaminsa, zai yi takarar gwamna

Wata Sabuwa: Ta sake kacamewa a APC, Sanata Adamu ya dakatar da dukkanin daraktocin jam'iyya
Wata Sabuwa: Ta sake kacamewa a APC, Sanata Adamu ya dakatar da dukkanin daraktocin jam'iyya. Hoto da Vanguardngr.com
Asali: UGC

A halin yanzu ya bazama gyara tsarin sakateriyar jam'iyyar inda ya mayar da ofishinsa kasa a maimakon hawa na uku da yake a baya.

A ranar 1 ga watan Afirilu, Adamu ya bayyana cewa akwai yuwuwar bincikar dukkan ma'aikatan sakateriyar ballantana daraktoci.

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa jam'iyyar ba za ta cigaba da amfani da tsoffin tsarika na baya ba wurin gudanar da ayyuka, inda ya kara da cewa mulkinsa ba zai lamunci gazawa ba ko kadan.

A ranar Juma'a, Vanguard ta tattaro cewa, sakamakon shawarar kwamitin, Adamu ya yanke shawarar dakatar da dukkanin daraktocin sakateriyar, kusan su takwas.

Wasu daga cikin daraktocin sun hada da na gudanarwa, tsari, jindadi da walwala, shari'a da yada labarai.

Wannan hukunci na Adamu za a iya cewa shi ne farko da aka taba yi a sakateriya jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Kwankwaso ya lale N30m, ya sayi fom din takarar shugaban kasa a jam'iyyar NNPP

A watan Yunin 2020, lokacin da tsohon shugaban jam'iyyar na kasa Kwamared Adams Oshiomhole ya ce zai sake tsara sakateriyar ta hanyar cire wadanda basu da wani abun yi a cikin gidan jam'iyyar.

A lokacin sai ya kawo wani tsari na tantance ma'aikata inda ya kori wasu daga ciki da suka dace.

APC ta sanar da ranar gudanar da zaben fidda gwanin dan takarar shugaban kasa

A wani labari na daban, majalisar zartaswa NEC ta jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta amince da ranar 30 da 31 ga Mayu matsayin ranakun gudanar da zaben fidda gwanin takarar shugaban kasa na zaben 2023.

Wannan na cikin sanarwar Sakataren yada labaran jam'iyyar na kasa, Barista Felix Morka, bayan taron majalisar NEC da ya gudana a Abuja ranar Laraba.

Barista Morka yace kuma ranar 18 Mayu za'a gudanar da zaben fidda gwanin gwamnoni, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Dalilin da yasa 'yan APC ke kara yawan mabiya a Najeriya, inji ministan Buhari

Asali: Legit.ng

Online view pixel