Kungiyoyi 150 sun tara miliyan N50m zasu saya wa Gwamna Zulum Fom na takara a APC

Kungiyoyi 150 sun tara miliyan N50m zasu saya wa Gwamna Zulum Fom na takara a APC

  • Wasu kungiyoyi masu zaman kansu a Borno sun fara karo-karo domin tara kudin da zasu saya wa gwamna Zulum Fom a APC
  • Mai magana da yawun gamayyar ƙungiyoyin, Mista Shettima, ya ce suna kira ga Zulum ya ayyana neman ta zarce a Ofishin gwamna
  • A cewarsa, al'umma suna bukatar mai girma gwamna ya cigaba da ayyukan da yake musu domin ya yi sun gani

Borno - Adadin ƙungiyoyi 150 kala daban-daban a jihar Borno sun fara karo-karo zasu haɗa Miliyan N50m da ake buƙata domin karbar wa Gwamna Zulum Fom din takara a zaɓen 2023.

Ƙungiyoyin na fafutukar tazarcen farfaesa Babagana Umaru Zulum a matsayin gwamnan Borno ƙarkashin inuwar APC, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Gamayyar ƙungiyoyin ta sanar da wannan aniya a wurin taron manema labarai da ya gudana a Maiduguri, babban birnin jihar Borno, ranar Jumu'a.

Kara karanta wannan

2023: Daga ƙarshe, Jam'iyyar APC ta faɗi gaskiyar abinda ya sa ta sanya kuɗin Fom Miliyan N100m

Gwamna Babagana Umaru Zulum.
Kungiyoyi 150 sun tara miliyan N50m zasu saya wa Gwamna Zulum Fom na takara a APC Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Mai magana da yawun gamayyar ƙungiyoyin, Umar Shettima, ya bayyana cewa suna fatan ganin Zulum ya cigaba da zama kujerarsa duba da ayyukan da ya zuba wa jihar a zangonsa na farko.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shettima shi ne shugaban ƙungiyar ma'aikatan jinya da masu karban haihuwa ta ƙasa reshen jihar Borno.

A jawabinsa ya ce:

"Gamayyar kungiyoyin ya hada da kungiyoyi masu rijista da kwararrun mutane a ɓangaren ilimi, lafiya, kasuwanci, sufuri, ƙungiyoyin mata da dai sauran su."
"Manufar mu ita ce mu tabbatar Farfesa Babagana Zulum ya cigaba da riƙe ofishinsa, ya yi mun gani, ya cimma nasarori fiye da tunani a kowane bangare na rayuwar al'umma ta yau da kullum a shekara uku."
"Muna kira gare shi ya sake neman wannan kujera ta gwamna a karo na biyu saboda ya cigaba da ayyukan Alherin da ya ɗakko yana yi wa al'ummar jihar Borno."

Kara karanta wannan

An samu ‘Yan siyasa 2 da suka saye fam a PDP, za su jarraba sa’a kan Zulum a 2023

Zamu haɗa kudin Fom - Shettima

Kakakin gamayyar kungiyoyin ya ce bisa ratsin kansu, sun yanke hukuncin tattara kudi domin saya wa Zulum Fom ɗin sha'awar takara.

"Bisa ganin damar mu, mun yanke siya wa Gwamna Zulum Fom ɗin sha'awar takara a babban zaɓen gwamnoni dake tafe a 2023."

Bayan haka ya roki al'ummar jihar Borno da su ba da na su tallafin zuwa asusun bankin da za'a ware, wanda nan gaba ƙaɗan zasu bayyana bayanansa.

A wani labarin kuma Rundunar yan sanda ta fallasa sunaye da Hotunan mutum 12 da take nema ruwa a jallo kan hannu a ta'addanci

Hukumar yan sandan ƙasar nan ta bayyana sunaye da hotunan wasu mutum 12 da take nema ruwa a jallo kan zargin ta'addanci.

Kakakin yan sanda, Muyiwa Adejobi, a wata sanarwa ya ce ana zargin mutanen da aikata manyan laifukan ta'addanci a Anambra.

Asali: Legit.ng

Online view pixel